Zai zama wauta a kame Sunday Igboho, Mailafia ga jami'an tsaro

Zai zama wauta a kame Sunday Igboho, Mailafia ga jami'an tsaro

- Wani masanin tattalin arziki a Najeriya ya shawarci sojojin Najeriya kan kame Sunday Igboho

- Ya bayyana karara cewa, Sunday Igboho a dokance yana da 'yancin aikata abinda yake aikatawa

- Ya kuma siffanta Sunday Igboho da jarumi mai fafutuka saboda kare al'ummar yankinsa

Wani tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Obadiah Mailafia ya shawarci jami’an tsaro cewa kada su kame mai fafutukar kafa haramtacciyar kasar Oduduwa ta Yarbawa Sunday Adeyemi ‘Igboho’.

Masanin tattalin arzikin ya fadi haka ne a ranar Laraba yayin wata hira da aka yi da shi a gidan Talabijin din Channels, ya kara da cewa Sunday yana fafutuka ne don mutanen sa.

KU KARANTA: Gwamnatin Najeriya roki 'yan kasa su daina amfani da robobi

Zai zama wauta a kame Sunday Igboho, Mailafia ga jami'an tsaro
Zai zama wauta a kame Sunday Igboho, Mailafia ga jami'an tsaro Hoto: tvcnews.tv
Asali: UGC

Ya bayyana karara cewa, a karkashin kundin tsarin mulkin kasa da na dokoki har ma da ka'idojin kasa da kasa da da'a na duniya mutane na da "'yancin kare kansu, don haka (hukumomin tsaro) a hikimance kada su kame Igboho,” in ji shi.

“Ya kamata su bar wannan mutumin; jarumi ne daga cikin mutanensa.”

Igboho ya yi fice a watan Janairun 2021 lokacin da ya ba da wa’adin mako guda ga makiyaya su tattara kwamusansu daga Ibarapa ta Jihar Oyo biyo bayan rikicin da ya addabi yankin.

KU KARANTA: Tsoron kada a bincikeshi, wani attajiri ya boye motarsa tsawon shekeru 40

A wani labarin daban, Gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, ya gargadi Sunday Igboho da wasu da ke neman kafa haramtacciyar kasar Yarbawa da su nisanci jiharsa, The Nation ta ruwaito.

Akeredolu ya ce mutanen Ondo sun zabi zama a Tarayyar Najeriya dunkulalliya kamar yadda aka tsara tun farkon kafa Najeriya.

Ya ce babu wani yanki na jihar, da aka sani kuma aka ayyana shi a matsayin jihar Ondo, da zai ba da izinin wani taro ko tashin hankali wanda zai iya ba da shawara ta kusa ko nesa, cewa mutane suna goyon bayan abin da ya kira 'rudani mai rudarwa.'

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel