Tsoron kada a bincikeshi, wani attajiri ya boye motarsa tsawon shekaru 40

Tsoron kada a bincikeshi, wani attajiri ya boye motarsa tsawon shekaru 40

- Wani shahararren attajiri ya boye mota tsawon shekaru 40 domin tsoron kada a bincike shi

- Attajirin ya boye motar a lokacin Ft Lt Jerry John Rawlings, tsohon shugaban kasar Ghana

- Tsabar jimawa da motar ta yi a boye, mutane suka saka mata Alhaji Agyaa Benz a matsayin suna

An gano wata mota kirar Mercedez Benz mallakar wani hamshakin attajiri a shekarun 1970 zuwa 1980, dan kasar Ghana mai suna Alhaji Agyaa, bayan kimanin shekaru 40 tana boye a cikin gareji.

A wani sako da shahararren dan jaridar wasanni, Saddick Adams ya wallafa a shafin Twitter, ya nuna cewa an gano motar ne a Techiman, babban birnin Techiman ta tsakiya da kuma yankin Bono ta gabas na kasar Ghana.

Wadanda suka taso a yankin sun san Alhaji Agyaa mai wadata ne kwarai, mashahuri kuma mai miliyoyin kudade da zai iya mallakar wannan Mercedes a yankin.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta ware zunzurutun kudi N1.13bn don gina hanyoyi 12

Tsoron kada a bincikeshi, wani attajiri ya boye motarsa tsawon shekeru 40
Tsoron kada a bincikeshi, wani attajiri ya boye motarsa tsawon shekeru 40 Hoto: @SaddickAdams
Asali: Twitter

An ce Alhaji Agyaa ya boye motar ne a lokacin mulkin Ft Lt Jerry John Rawlings wanda ke da idanun dirar mikiya a kan duk wanda yake da dukiya fiye da kima don tabbatar da cewa ba sa sace kudin kasa

An boye motar ne a wani gareji hadin gida na musamman wanda Alhaji Agyaa ya gina don boye motar kuma har yanzu ba’a taba bude shi ba.

Rahotanni sun nuna cewa motar ana kiranta da suna Alhaji Agyaa Benz a lokacin saboda a da tana matsayin abin tarihi ne wanda jama'ar gari ke magana akai a wancan lokacin.

KU KARANTA: Kotu ta bada umarnin tsawaita wa'adin rajistar NIN zuwa watanni biyu

A wani labarin daban, Gwamnatin Najeriya ta bukaci 'yan kasar su daina amfani da robobi su koma amfani da abubuwa masu saurin narkewa domin rage illolin da robobin ka iya haifarwa ga muhalli, BBC ta rahoto.

Mataimakin shugaban hukumar da ke kare muradan masu sayayya Barrister Babatunde Irukera ya ce tuni wasu jihohin irinsu Kano da Legas suka rungumi wannan tsarin na yadda za su rage amfani da robobi da yadda kuma za a rika sake amfani da robobin da aka yi amfani da su a baya.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel