'Yan Bindiga sun hallaka wani Sufeton 'yan sanda, Sun babbaka motarsu a Delta

'Yan Bindiga sun hallaka wani Sufeton 'yan sanda, Sun babbaka motarsu a Delta

- Wasu 'yan bindiga sun farmaki yan sanda ya yin da suke tsakar sintiri a garin Ashaka, karamar hukumar Ndokwa, jihar Delta

- Maharan sun hallaka wani ƙaramin sufeta sannan suka babbaka ma motar yan sandan wuta.

- Jami'i mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Delta, Mr. Bright Edafe, ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma yace an kashe musu jami'i daya.

Wasu yan bindiga sun farmaki yan sanda ya yin da suke sintiri a garin Ashaka, karamar hukumar Ndokwa ta gabas a jihar Delta.

KARANTA ANAN: Masu Baburan Adaidaita Sahu Sun Shiga Yajin Aiki a Maiduguri

Yan bindigan sun caka ma ɗaya daga cikin yan sandan wuƙa wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsa kuma suka jikkata wasu sannan suka babbaka ma motar da yan sandan ke sintiri da ita wuta.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa maharan sun kori 'yan sandan da tsiya kuma suka yi gaba da makaman su.

Lamarin dai ya faru ne a ranar Talata, a wani yanki na garin Ashaka.

'Yan Bindiga sun hallaka wani Sufeton 'yan sanda, Sun babbaka ma motar su Wuta a Delta
'Yan Bindiga sun hallaka wani Sufeton 'yan sanda, Sun babbaka ma motar su Wuta a Delta Hoto: @PoliceNG_News
Asali: Twitter

Duk da cewa babu wani cikakken bayani akan abunda yafaru zuwa yanzun, amma an tabbatar da mutuwar sufeta mai suna Musa wanda suka caka ma wuƙa.

Wata majiya da ta umarci a sakaya sunanta ta bayyana ma jaridar Vanguard cewa: "Yan bindigan sun taho ne akan mota, suka farmaki yan sandan da suka fito sintiri a yankin."

KARANTA ANAN: Majalisar Dattijai ta amince da wani Naɗin da Buhari ya turo mata na wani Babban Muƙami

Da aka tuntuɓi mai magana da yawun rundunar yan sanda, Mr. Bright Edafe, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce an kashe musu ɗan sanda guda ɗaya.

Ya kuma ƙara da cewa hukumar su ta tura jami'anta inda lamarin ya faru don gudanar da bincike.

A wani labarin kuma Rundunar Yan sanda na neman wasu Mutane 18 Ruwa a jallo a Jihar Ebonyi

Yan sandan sun bayyana cewa suna zargin mutanen da hannu a tayar da tashe-tashen hankula tsakanin ƙabilu.

Jami'i mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar ne ya bayyana haka a wani saƙo da ya aike ma yan Jarida ranar Talata.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban- daban.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77.

Asali: Legit.ng

Online view pixel