Dan Allah ka farka, kasar nan na wargajewa - Baba Ahmed ga Buhari

Dan Allah ka farka, kasar nan na wargajewa - Baba Ahmed ga Buhari

- Kungiyar Dattawan Arewa ta soki Shugaban kasa Muhammadu Buhari

- A cewar kakakin kungiyar, shugaban kasar na tafiyar hawainiya sosai wajen magance wasu matsalolin kasar

- Ya ce zai fada wa Buhari cewa kasar na rugujewa idan ya samu damar tattaunawa da shi

A wani abin da zai haifar da martani daban-daban daga 'yan Nigeria, an nemi Shugaba Muhammadu Buhari da ya gaggauta daukar mataki kafin abubuwa su tabarbare sosai a kasar.

Kakakin kungiyar dattawan Arewa (NEF), Hakeem Baba-Ahmed ne ya yi kiran.

A cewarsa, Shugaba Muhammadu Buhari na tafiyar hawainiya sosai.

KU KARANTA KUMA: Ina durkusawa tare da mika kai ga mijina - Shugabar kasar Tanzania ta fadawa Mata a bidiyo

Dan Allah ka farka, kasar nan na wargajewa - Baba Ahmed ga Buhari
Dan Allah ka farka, kasar nan na wargajewa - Baba Ahmed ga Buhari Hoto: @MBuhari
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ya bayyana hakan ne lokacin da yake magana a gidan talabijin na Arise a ranar Laraba, 24 ga Maris.

Da yake ci gaba da magana, ya ce zai fada wa shugaban kasar zuciyarsa idan ya samu damar zama da shi.

Ya ce zai fada wa shugaban kasar ya farka ga nauyin da ke kansa kasancewar kasar ta dauki hanyar rugujewa.

Ya ce:

"Idan na samu damar tattaunawa da shugaban kasar, zan ce: 'Yallabai, don Allah ka farka ka fuskanci zahiri, ƙasar nan tana wargajewa."

“Me yasa bamu da tsaro? Me ya sa ’yan Najeriya ba za su magance matsalar ta’addanci da satar mutane ba? Wadannan abubuwan biyu, shekaru uku da suka gabata babu su. Shin wani yana yin waɗannan tambayoyin? Shin kuna da wannan jituwa a cikin hukumomin tsaron ku? Shin kuna da hanyar gano hakan saboda bamu da lokacin da zaka gyara kasar nan a lokacin da ka dama kuma a yanda kake tafiya, kana jinkiri sosai kuma mutane sun fara yanke kauna da gwamnatin ka kuma wannan shine dalilin da ya sa ka ga mutane na fadin cewa ba ma son kasancewa cikin Najeriya."

KU KARANTA KUMA: Dole ku shafa mana lafiya a 2023, PDP ta aika sakon gargadi ga APC

A wani labarin, fadar shugaban kasa ta yi watsi da rahotannin cewa akwai rashin jituwa tsakanin shugaba Muhammadu Buhari da babban jigon jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

A jawabin da mai magana da yawun shugaban, Garba Shehu, ya saki ranar Laraba, ya ce akwai alaka mai karfi tsakanin Buhari da Tinubu musamman wajen ganin cigaban jam'iyyar All Progressives Congress, APC.

A cewar Garba Shehu, rahotannin da ake yadawa cewa akwai rahin jituwa cikin Buhari da Tinubu, aikin wasu miyagin yan jarida ne.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng