Gwamnatin Buhari ta ware zunzurutun kudi N1.13bn don gina hanyoyi 12

Gwamnatin Buhari ta ware zunzurutun kudi N1.13bn don gina hanyoyi 12

- Gwamnatin tarayya ta ware makudan kudade domin aikin gina hanyoyi a fadin Najeriya

- Gwamnatin ta bayyana aikin da cewa, dukkan jihohin kasar za su ci gajiyarsa ciki har da FCT

- Ministan Ayyuka da Gidaje ya bayyana ana bukatar karin wasu kudaden don cimma burin

Gwamnatin tarayya a ranar Talata ta ce ta ware N1,134,690,048,000.76 a matsayin babban kason farko na gina hanyoyi 12, The Nation ta ruwaito.

Ministan Ayyuka da Gidaje, Mista Babatunde Fashola, wanda ya bayyana haka, ya ce an zabi hanyoyin ne domin tabbatar da shiyyoyin siyasa shida na kasar sun ci gajiyar aikin.

Ya kara da cewa Gwamnatin Tarayya tuni ta fara aiwatar da kwangiloli sama da 700, wadanda suka hada da gyara da sake gina hanyoyi sama da kilomita 13,000 da gadoji a fadin jihohi 36 na tarayyar kasar da Babban Birnin Tarayya (FCT).

KU KARANTA: Saura kiris a fara biyan masu aikin sufuri tallafin kudi na 'Survival Fund'

Gwamnatin Buhari ta amince da kashe N1.13bn don gina hanyoyi 12
Gwamnatin Buhari ta amince da kashe N1.13bn don gina hanyoyi 12 Hoto: independent.ng
Asali: UGC

Fashola ya fadi haka ne a lokacin da yake gabatar da bayani ga Ma'aikatar Gudanarwa da Ci Gaban Manyan Hanyoyi, inda ya ce sakamakon girman aikin, akwai bukatar kudade don daukar nauyin ayyukan don kammalawa da kuma kula da su.

Har ila yau, akwai bukatar samar da kudaden gudanar da wasu ayyuka na hadin gwiwa kamar gadoji masu daukar nauyi, gidajen ajiye motocin daukar kaya da sauran kayayyakin da suka fi dacewa da shirin kasuwanci na kamfanoni masu zaman kansu, in ji Ministan.

KU KARANTA: Ahmad Lawan: Ba tsige Buhari ne zai kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya ba

A wani labarin, A kokarin farfado da tattalin arzikin kasa, gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a Najeriya ta karbo bashin naira biliyan daya domin taimakawa masu kananan masana'antu, BBC ta ruwaito.

An karbo bashin ne ta hannun bankin masana'antu karkashin Ma'aikatar kasuwanci masana'antu da zuba hannayen jari ta kasar.

Adeniyi Adebayo na ma'aikatar ne ya bayyana hakan yayin wani shiri na karfafawa kananan masana'antu da aka yi.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel