Buhari ya karbo bashi daga waje don tallafawa masu kananan masana'antu
- Gwamnatin Najeriya ta karbo bashin makudan kudade don tallafawa kananan masana'antu
- Gwamnatin ta bayyana hakan a matsayin kokarin farfado da tattalin arzikin kasar da ya suma
- An karbo bashin ne karkashin ma'aikatar kasuwanci, masana'antu da zuba hannun jari ta kasar
A kokarin farfado da tattalin arzikin kasa, gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a Najeriya ta karbo bashin naira biliyan daya domin taimakawa masu kananan masana'antu, BBC ta ruwaito.
An karbo bashin ne ta hannun bankin masana'antu karkashin Ma'aikatar kasuwanci masana'antu da zuba hannayen jari ta kasar.
Adeniyi Adebayo na ma'aikatar ne ya bayyana hakan yayin wani shiri na karfafawa kananan masana'antu da aka yi.
KU KARANTA: Bakuwar cuta a Kano: FG ta aika da rundunar taimakon gaggawa zuwa Kano
Cikin wata sanarwa Adebayo ya ce bashin zai taimakawa ninkin masana'antun ta yadda zai iya bayar da taimakonsa ga masu kananan sana'o'i wanda hakan ake sa ran zai karfafa tattalin arzikin kasar.
A cewarsa wannan wani mataki ne na farfado da komadar tattalin arzikin kasar da ya jikkata da kuma tabbatar da cewa ya ci gaba da dorewa.
KU KARANTA: Fayose ga Buhari: Ka bai wa 'yan Najeriya kunya da alkawuranka
A wani labarin daban, Karamar Ministar Masana'antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Mariam Katagum, a ranar Litinin ta ce tun daga farkon wadanda suka fara cin gajiyar shirin a ranar 17 ga Janairun 2021, an amince da biyan jimilar mutane 155,920 da za su ci gajiyar shirin Survival Fund a fannin sufuri.
Wannan na fitowa ne daga wata sanarwar babban mataimaki na musamman ga mataimakin shugaban kasa kan harkokin yada labarai ya fitar a wasu tarurruka da aka gudanar na shirin, jaridar Punch ta ruwaito.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng