Saura kiris a fara biyan masu aikin sufuri tallafin kudi na 'Survival Fund'

Saura kiris a fara biyan masu aikin sufuri tallafin kudi na 'Survival Fund'

- Gwamnatin tarayya ta amince da biyan wadanda suka cika shirin tallafin Survival Fund

- An ruwaito cewa, za a fara biyan sama da mutane 150,000 na shirin a fannin kasuwacin safara

- An kuma bayyana cewa, kashi 43 na wadanda suka ci gajiyar shirin na Survival Fund mata ne

Karamar Ministar Masana'antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Mariam Katagum, a ranar Litinin ta ce tun daga farkon wadanda suka fara cin gajiyar shirin a ranar 17 ga Janairun 2021, an amince da biyan jimilar mutane 155,920 da za su ci gajiyar shirin Survival Fund a fannin sufuri.

Wannan na fitowa ne daga wata sanarwar babban mataimaki na musamman ga mataimakin shugaban kasa kan harkokin yada labarai ya fitar a wasu tarurruka da aka gudanar na shirin, jaridar Punch ta ruwaito.

Sanarwar ta bayyana cewa, “Jimillar mutane 155,920 da za su ci gajiyar shirin a fannin sufuri ya zuwa yanzu an amince da a biya su yayin da har yanzu mutum 9,109 ke jiran tantacewa don biya.

KU KARANTA: Fayose ga Buhari: Ka bai wa 'yan Najeriya kunya da alkawuranka

Saura kiris a fara biyan masu aikin sufuri tallafin kudi na 'Survival Fund'
Saura kiris a fara biyan masu aikin sufuri tallafin kudi na 'Survival Fund' Hoto: survivalfund.gov.ng
Asali: UGC

"Ministar ta kara da cewa adadin da za a lissafa ya kai kimanin 19,689 amma ta lura cewa 22% cikin 100% na matan da za su ci gajiyar shirin ne kawai aka samu saboda yanayin kasuwancin safarar."

A cewar sanarwar, ministar ta lura cewa bangaren ilimi kadai yana da adadin wadanda suka cika kusan 850,000 a cikin mako guda da aka sake bude kafar, idan aka kwatanta yakai kusan rabin adadin lokacin da aka fara bude kafar tsawon makonni shida.

An sake ruwaito ta tana cewa zuwa yanzu, 43% cikin 100% na wadanda suka ci gajiyar shirin na Survival Fund mata ne.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe shugaban wasu Fulani a jihar Kaduna

A wani labarin daban, Rundunar Shugaban kasa kan Korona ta ce ta karbi allurai 300,000 na rigakfin Oxford-AstraZeneca daga kamfanin MTN Najeriya, ta ruwaito.

Da yake magana a taron na kasa, Shugaban PTF kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ya ce: “Jiya Lahadi, 21 ga Maris 2021, PTF ta karbi allurai 300,000 na rigakafin Oxford-AstraZeneca daga MTN Najeriya.

"An tabbatar da wannan tare da godiya yayin da muke karfafawa sauran kishiyoyi da su bada gudummawa wajen yakar Korona" in ji Boss Mustpaha.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel