Ahmad Lawan: Ba tsige Buhari ne zai kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya ba
- Shugaban majalisar dattawa yayi fatali da kudurin da ke neman a tsige shugaba Buhari
- Ahmad Lawan ya bayyana cewa, tsige shugaban ba zai kawo karshen matsalar tsaro ba
- Ya bukaci shugaban - ta bakin wakilinsa - da ya kara dagewa wajen magance matsalar
Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan, ya yi watsi da batun tsige Shugaba Muhammadu Buhari da Majalisar Dokoki ta Kasa ta yi game da rashin tsaro a kasar, yana mai cewa irin wannan matakin ba zai magance matsalar ba, The Guardian ta ruwaito.
Ya yi wannan tsokaci ne yayin wasan karshe na gasar kwallon kafa ta Filato ta Arewa ta farko, na hadin kai da sulhu wanda Istifanus Gyang, mai wakiltar gundumar Filato ta Arewa a Majalisar Dattawa ya shirya.
KU KARANTA: Wata kungiyar Fulani ta yi ikrarin kai wa gwamnan Benue hari, ta ce ta so kashe shi ne
Lawan, wanda Sanata mai wakiltar Gundumar Benue ta Arewa maso Gabas, Gabriel Suswan ya wakilta, ya ce:
“Tsige Shugaba Buhari ba shi ne abin da Majalisar Tarayya ta sa a gaba ba domin hakan ba zai iya magance matsalar rashin tsaro a kasar ba. Sai dai ana bukatar babban kwamandan ya dauki mataki don kawar da tsoron ‘yan Nijeriya.”
A cewar Suswan, duk wani abin da ya faru na rashin tsaro da ya ci gaba, kamar abin da kasar ke gani a yau, gazawar bangaren zartarwa ne, walau a matakin jiha ko na kasa.
"Abin da muke fuskanta a yau na bukatar jajircewa daga bangaren zartarwa amma hakan na nan tafe."
Ya tunatar da Buhari cewa shi Shugaba ne na kowa, don haka, ya kamata, ya yi aiki don amfanin 'yan Nijeriya.
Suswan yace,
“Mu a majalisar kasa muna ci gaba da yin iya kokarinmu. Mun zartar da kuduri da shawarwari, amma yawancinsu ba a mutunta su ba. Shugaban yana bukatar ya fifita fifikon Najeriya a kan kowacce,”
Suswan ya nuna goyon baya ga kudiri don kafa hukuma ta musamman ta sojoji, wanda a kwanan nan ya raba kan Majalisar ta Dattawa.
Sai dai, ya ce kudirin, wanda ke neman karbar ikon nada shugabannin sojoji, daukar su aiki da kuma yi musu ritaya ta hannun shugaban kasa, ba shi da muhimmanci kamar tura sojoji don fatattakar masu tayar da kayar baya.
KU KARANTA: Dattijon kasa: Ana fakewa da matsalar makiyaya ana raba kan 'yan Arewa
A wani labarin daban, Shugaban riko na kwamitin tsare-tsaren babban taron kasa na jam'iyyar APC kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya ce jam'iyyar na kokarin ganin ta ci gaba da mulki a kalla na tsawon shekaru 32, Daily Nigerian ta ruwaito.
Mista Buni ya bayyana hakan ne lokacin da yake kaddamar da kwamitin tuntuba da dabaru na jam’iyyar na mambobi 61, a Sakatariyar APC ta Kasa, da ke Abuja, a ranar Talata.
A cewarsa, ya kamata jam'iyyar ta kasance a kan mulki don ci gaba da samar da romon dimokiradiyya da take gabatarwa tun daga shekarar 2015.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng