Dattijon kasa: Ana fakewa da matsalar makiyaya ana raba kan 'yan Arewa

Dattijon kasa: Ana fakewa da matsalar makiyaya ana raba kan 'yan Arewa

- Wani sanata daga jihar Nasarawa ya bayyana rashin jin dadinsa ga siyasantar da lamarin makiyaya

- Yace ana amfani da sunan makiyaya ne kadai don a raba kan al'ummar yankin arewacin kasar

- Ya kuma nuna cewa, arewa aka sani da kiwo ba kudu ba, kuma ba a yiwa makiyaya adalci ba

Dattijon Arewa kuma dan majalisar dattawa daga Nassarawa Sanata Abdullahi Adamu, ya ce ana kokarin fakewa da sunan hare-haren da ake zargin makiyaya na kaiwa wasu jihohin kasar ne domin raba kan al'ummar arewa.

Yayin wata hira da BBC Sanatan, ya ce rikicin ya samo asali ne sakamakon toshe hanyoyi ko burtalin da suke bi, da kuma dazukan da aka kebe saboda kiwo, sannan aka gagara samar da wani shiri don ganin sun gudanar da harkokinsu.

''Ana neman dalili ne domin bata sunan makiyaya don a la'ance su, ana maganar kiwo wake maganar kudu?, ai kowa ya san kiwo a arewa yake, don haka wuta ce ake kunnowa domin ganin an raba kan alummar arewa'' a cewar Sanatan.

KU KARANTA: Zulum da sauran gwamnoni 4 da tsageru suka taba kaiwa hari a Najeriya

Dattijon kasa: Ana fakewa da matsalar makiyaya ana raba kan 'yan Arewa
Sanata Adamu Abdullahi, Sanata mai wakiltar Nasarawa ta yamma, dan jam'iyyar APC | Hoto: BBC
Asali: UGC

Ya jaddada cewa, matukar ana son kawo karshen matsala, to dole ne gwamnati ta fahimci hadarin da ke cikin bari ana yin kiwo sakaka a fili, hasalima idan ta fahimci haka ya kamata ta samarwa makiyaya wata hanya da za su rika gudanar da harkokinsu.

Ya kuma bayyana yadda alakar Hausa/Fulani take a arewacin kasar da kuma yadda al'ummar kudu ke wa yankin na arewa kudin goro.

A cewarsa ''Dole mu so juna, mutumin kudu ai bai san wata kabila Hausa Fulani ba, a ganinsa duk a dunkule muke, wannan bai isa ba, yanzu kuma so ake a raba kan Hausa da Fulanin ma''.

Hare-hare a Najeriya na kara kamari, wanda hakan ya bayyana a idon duniya sakamakon yawan sace daliban makaranta da aka yi a baya-bayan nan.

Matsalar sace-sacen dalibai dai ta kara karfi a Najeriya ne daga hawan shugaban kasa mai ci Muhammadu Buhari.

KU KARANTA: Gwamnatin Najeriya roki 'yan kasa su daina amfani da robobi

A wani labarin, Wata kungiyar Fulani da ke ikirarin kare muradin Fulanin (FUNAM), ta ce ita ke da alhakin yunkurin kashe Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue, PM News ta ruwaito.

A cikin wata sanarwa da aka bai wa manema labarai, wanda aka yi kuskuren rubuta sunan Ortom sau da yawa, kungiyar ta ce manufarta ita ce kashe Ortom.

Ta sha alwashin hallaka Ortom, saboda kamar yadda ta yi ikirarin, yana adawa da Fulani.

"Mayakanmu sun kai wannan harin na tarihi don aika babban sako ga Ortum da wadanda suka hada kai dashi", kungiyar ta yi ikirarin a wata sanarwa da Umar Amir Shehu ya sanya hannu.

“Duk inda kuka kasance, matukar kun nuna adawa da sha'awar Fulani na dogon zango, to za mu durkushe ku.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel