Wata kungiyar Fulani ta yi ikrarin kai wa gwamnan Benue hari, ta ce ta so kashe shi ne

Wata kungiyar Fulani ta yi ikrarin kai wa gwamnan Benue hari, ta ce ta so kashe shi ne

- Wata kungiyar Fulani ta bayyana karara cewa, ita ta kai wa gwamnan jihar Benue hari

-Kungiyar ta yi alwashin kashe gwamna Ortom nan ba da dadewa, kawai dama ake jira

- Kungiyar ta kuma gargadi wasu jihohin kudu dake kira da masu mummunar adawa da Fulani

Wata kungiyar Fulani da ke ikirarin kare muradin Fulanin (FUNAM), ta ce ita ke da alhakin yunkurin kashe Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue, PM News ta ruwaito.

A cikin wata sanarwa da aka bai wa manema labarai, wanda aka yi kuskuren rubuta sunan Ortom sau da yawa, kungiyar ta ce manufarta ita ce kashe Ortom.

Ta sha alwashin hallaka Ortom, saboda kamar yadda ta yi ikirarin, yana adawa da Fulani.

"Mayakanmu sun kai wannan harin na tarihi don aika babban sako ga Ortum da wadanda suka hada kai dashi", kungiyar ta yi ikirarin a wata sanarwa da Umar Amir Shehu ya sanya hannu.

“Duk inda kuka kasance, matukar kun nuna adawa da sha'awar Fulani na dogon zango, to za mu durkushe ku.

KU KARANTA: Ya kamata Buhari ya dage da addu'a, na hango rudani a nan gaba, in ji wani Fasto

Wata kungiyar Fulani: Mun so kashe Ortom, mu muka kai masa hari
Wata kungiyar Fulani: Mun so kashe Ortom, mu muka kai masa hari Hoto: koko.ng
Asali: UGC

“Wannan gargadi ne karara. Muna fatan wadanda suka dauke mu ba a bakin komai ba za su samu sakon da ba za a iya musantawa ba.

“Niyyar mu babu shakka: KASHE SHI. Wannan manufa za ta cika wata rana kuma nan ba da jimawa ba ”.

Baya ga tsoratar da Ortom, kungiyar ta kuma aika wani gargadi mai ban mamaki zuwa jihohin kudu, tana mai cewa wadanda suka kashe mambobinta su ma suna zuwa domin su.

“Muna gargadin masu hadin gwiwa dake adawa da Fulani a duk fadin Najeriya: ZAMU SAMO KU ba tare da la’akari da buyayyun wuraren ku ba.

“Mun bayyana karara, duk wata jiha ko daidaikun mutane da ke adawa da RUGA za mu fuskance su. Duk wata jiha ko mutum daya da ke adawa da kiwo, za mu same ku.

"Ku yi magana game da kiwo da RUGA koda akan intanet ne: Mayakanmu na nan za su same ku kuma su gyara muku zama.

“A cikin 'yan watanni masu zuwa, FUNAM za ta kai hare-hare kan wasu mutane da dukiyoyin jihohi ko na mutanen da suka shahara da yakin nuna kyamar Fulani.

”Za mu yi farautar ku a gidajenku, a wuraren aikinku, a cikin motarku, a titunanku. Lokacin da ya dace."

KU KARANTA: 'Yan ta'addan Boko Haram sun hallaka sojojin Kamaru a Najeriya

A wani labarin daban, Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta bayyana harin da 'yan bindiga suka kai wa gwamnan Jihar Benue a matsayin "abin kidimarwa". BBC Hausa ta ruwaito.

A jiya Asabar ne wasu 'yan bindiga suka kai wa tawagar Gwamna Samuel Ortom hari a gidan gonarsa da ke kan hanyar Makurdi zuwa Gboko a jihar ta Benue.

Cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar kuma Gwamnan Jihar Ekiti Kayode Fayemi ya fitar a yau Lahadi, NGF ta taya Ortom alhini game da harin da ta ce "na tsoro ne kum na keta".

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel