Fayose ga Buhari: Ka bai wa 'yan Najeriya kunya da alkawuranka

Fayose ga Buhari: Ka bai wa 'yan Najeriya kunya da alkawuranka

- Tsohon gwamnan jihar Ekiti ya caccaki shugaba Buhari kan karbar sabbin masu sauya sheka

- Fayose ya bayyana cewa, 'yan Najeriya sun kunyata da rashin cika alkawuran shugaba Buhari

- Ya kuma bayyana cewa, bai kamata shugaba Bhari yake karbar 'yan gantalin siyasa a fadarsa ba

Tsohon Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose a daren Litinin ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya kunyata ‘yan Najeriya, The Nation ta ruwaito.

Ya kuma bayyana cewa 'yan Najeriya sun yanke kauna kan alkawuran da ya dauka.

Fayose, a shafinsa na Twitter, ya soki ziyarar tsohon gwamnan Ogun, Gbenga Daniels da tsohon kakakin majalisar Dimeji Bankole ga Buhari, yana mai bayyana su a matsayin "'yan gantalin siyasa".

KU KARANTA: Gandollar: Idan wani abu ya same ni, a tuhumi Ganduje, Jaafar Jaafar ga IGP

Fayose ga Buhari: Ka bai wa 'yan Najeriya kunya da alkawuranka
Fayose ga Buhari: Ka bai wa 'yan Najeriya kunya da alkawuranka Hoto: withinnigeria.com
Asali: UGC

Ya ce: "'Yan Najeriya ba su da sha'awar Shugaban kasa mai karbar 'yan gantali a cikin Villa. Sun fi son zaman lafiyarsu, musamman tsaro.

“Suna so su ga shugaban kasa wanda ke da kwazo wajen tafiyar da al’amuran kasar, maimakon karbar 'yan siyasar da aka sake amfani da su.

“Mafi mahimmanci, 'yan Nijeriya ba su da sha’awar adadin ‘yan siyasar da suka sauya sheka zuwa APC, wacce tuni ta riga ta mutu.

"Ya kamata Shugaban kasa ya ba da kansa ga 'yan Najeriya wadanda za su iya taimaka mana wajen magance matsalolin arziki da tsaro da muke fuskanta da sauransu."

"Fiye da komai, ina fatan Shugaban kasa ya san yadda 'yan Najeriya ke jin takaici game da shi da kuma rashin cika alkawuransa."

KU KARANTA: Kamfanin MTN ya bai wa Najeriya gudunmawar alluran Korona guda 300,000

A wani labarin daban, Wani tsohon mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar dattijai kuma jigo a jam'iyyar APC, Sanata Abu Ibrahim, ya ce Najeriya za ta zauna lafiya a karkashin Asiwaju Bola Tinubu, idan aka zabe shi a matsayin Shugaban kasa a zaben 2023.

Tsohon sanatan dan asalin jihar Katsina yayi wannan maganan ne a karshen mako a Abuja yayin kaddamar da kungiyar nuna goyon bayan Bola Tinubu (BTSO), The Nation ta ruwaito.

Ya nuna goyon baya ga masu tallata shugabancin Bola Tinubu a 2023, yana mai cewa ya san Shugaban na APC na Kasa sama da shekaru 20.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.