Gandollar: Idan wani abu ya same ni, a tuhumi Ganduje, Jaafar Jaafar ga IGP

Gandollar: Idan wani abu ya same ni, a tuhumi Ganduje, Jaafar Jaafar ga IGP

- Mawallafin jaridar Daily Nigerian ya kai karar Ganduje wajen Sufeto-Janar na 'yan sanda

- Ya bayyana cewa, Ganduje na shirin cutar dashi a wasu jawaban da yayi a makon da ya gabata

- Ya roki Sufeto-Janar din da ya zargi gwamna Ganduje matukar wani abu mummuna ya same shi

Biyo bayan sabuwar barazanar da ake yi wa rayuwarsa, mawallafin jaridar Daily Nigerian, Jaafar Jaafar, ya kai kara ga Sufeto-Janar na ’yan sanda, Mohammed Adamu, yana cewa a dauki mataki kan Gwamna Abdullahi Ganduje idan wani abu ya same shi.

A watan Oktoba na shekarar 2018, Jaafar ya wallafa wasu faya-fayen bidiyo da ke nuna yadda gwamnan ke sakama daloli a aljihu da ake zaton cin hanci ne daga ‘yan kwangila da ke gudanar da ayyuka daban-daban da gwamnatin jihar ta bayar.

Tuni dai gwamnan ya musanta faya-fayan bidiyon, yana mai bayyana su a matsayin wadanda aka shirya kamar fim.

Amma a wata hira da ya yi da Sashin Hausa na BBC a ranar Juma’a, 19 ga Maris, Mista Ganduje ya bayyana cewa gwamnatin jihar na shirin yin maganin wadanda ke bayan bidiyon.

KU KARANTA: Iyayen dalibai sun bai wa El-Rufa'i wa'adin awanni 48 ya dawo musu da 'ya'yansu

Gandollar: Idan wani abu ya same ni, a tuhumi Ganduje, Jaafar Jaafar ga IGP
Gandollar: Idan wani abu ya same ni, a tuhumi Ganduje, Jaafar Jaafar ga IGP Hoto: nairaland.com
Asali: UGC

Dangane da sabon barazanan, Mista Jaafar, ta hannun lauyansa, Barista Abdullahi Gumel, ya rubuta wa Sufeto-Janar na 'yan sanda yana mai nuna masa cewa gwamnan da magoya bayansa suna shirin cutar da mawallafin.

Lauyan ya bayyana cewa Jaafar Jaafar da iyalansa na rayuwa cikin fargaba ba ma a iya jihar Kano ba, har ma a babban birnin tarayya Abuja da sauran sassan kasar.

Ya kuma ce, barazanar baya da rayuwa cikin tsoro bai isa haka ba, "a kwanan nan Mista Ganduje ya nuna cewa shi da magoya bayansa suna kulla makirci ta hanyar "yin maganin" abokin huldarmu.

"Ganduje ya yi wannan bayanin ne a wani shahararren shirin BBC Hausa mai suna "A Fada A Cika" wanda aka gabatar a ranar 19 ga Maris 2021. Ya dage kan cewa ba zai bayyana shirin na su ba duk da wata dama ta fayyace abin da yake nufi.

Lauyan ya zargi gwamna Ganduje da zugi da harzuka magoya bayansa su cutar da Mista Jaafar.

Karshe ya bukaci Sufeto-janar na 'yan sanda da ya kokarta wajen ganin Jaafar Jaafar ya kubuta daga mugun nufin gwamnan.

KU KARANTA: A karkashin mulkin Tinubu ne kadai Najeriya za ta daidaita, in ji wasu manyan arewa

A wani labarin daban, Babbar Kotun Jihar Kano da ke zamanta a Titin Miller na Unguwar Bompai, a yau Litinin ta ci gaba da sauraron shari’ar bidiyon zuba daloli a cikin aljihu da ake zargin an nado gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje yana yi.

A shekarar 2018 aka wallafa wani bidiyon gwamna Ganduje yana sanya daloli a cikin aljihu wanda ake zargin cin hanci ne daga wani dan kwangila a Jihar, lamarin da makarraban gwamnan suka ce bidiyon ba sahihi ba ne kuma an yi hakan ne kurum dan a bata shi.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.