A karkashin mulkin Tinubu ne kadai Najeriya za ta daidaita, in ji wasu manyan arewa

A karkashin mulkin Tinubu ne kadai Najeriya za ta daidaita, in ji wasu manyan arewa

- Wani tsohon sanatan jihar Katsina ya bayyana ra'ayinsa game da bai wa Bola Tinubu shugabanci a 2023

- Sanatan ya bayyana cewa, a karkashin mulkin Bola Tinubu ne kadai Najeriya za ta zauna lafiya

- Hakazalika wani jigo a gwamnatin jihar Neja shima ya goyi bayan maganar tsohon sanatan

Wani tsohon mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar dattijai kuma jigo a jam'iyyar APC, Sanata Abu Ibrahim, ya ce Najeriya za ta zauna lafiya a karkashin Asiwaju Bola Tinubu, idan aka zabe shi a matsayin Shugaban kasa a zaben 2023.

Tsohon sanatan dan asalin jihar Katsina yayi wannan maganan ne a karshen mako a Abuja yayin kaddamar da kungiyar nuna goyon bayan Bola Tinubu (BTSO), The Nation ta ruwaito.

Ya nuna goyon baya ga masu tallata shugabancin Bola Tinubu a 2023, yana mai cewa ya san Shugaban na APC na Kasa sama da shekaru 20.

Ibrahim ya bayyana Asiwaju Tinubu a matsayin dan Najeriyar da ke da manufa kuma babban jagora wanda ke da sha'awar gano kwarewa da kwazon matasa masu tasowa ya jagorance su zuwa mukamai.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: Gobara ta yi kaca-kaca da babbar kasuwar Katsina

A karkashin mulkin Tinubu ne kadai Najeriya za ta daidaita, in ji wani tsohon Sanata
A karkashin mulkin Tinubu ne kadai Najeriya za ta daidaita, in ji wani tsohon Sanata Hoto: nigeriainfo.fm
Asali: UGC

“Na san Asiwaju Tinubu sosai. Mun kasance abokai fiye da shekaru 20. Shi mutum ne mai himma da kwazo. Shi ne mai gina hadin kai kuma ginshikin hadin kan Najeriya. Ina ganin Najeriya za ta zauna lafiya a hannunsa.”

Har ila yau, Sakataren Gwamnatin Jihar Neja (SSG), Farfesa Mohammed Kuta Yahaya, ya jinjina wa Shugaban Jam’iyyar ta APC na kasa saboda kwarewa a jagoranci.

Ya lura cewa tsohon gwamnan na Legas ya jagoranci ‘yan Najeriya da yawa a mukamai daban-daban na shugabanci a fadin kasar.

Yahaya, wanda shi ne Shugaban bikin rantsarwar, ya jaddada cewa babu wani shugaba a Najeriya da ya ke da kwazo kamar na Asiwaju Tinubu.

“Shin akwai wani dan Najeriya a fagen siyasa ko kuma harkar kasuwanci da ya jagoranci shugabanni masu tasowa kamar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu?

Yahaya ya ce "Ya kamata mu kirkiro wani Bola Ahmed Tinubu a kowane shiyya na shiyyoyi shida na siyasar kasar nan, kuma za ku ga ba za a samu talauci da rashawa a Najeriya ba."

Mai gabatar da taron kuma Kodinetan kungiyar na BTSO, Abubakar Kuso ya ce takarar kujerar Shugaban kasa a zaben 2023 na bukatar mutum mai hangen nesa kamar Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa wato Tinubu.

“Ni saurayi ne kuma mai matukar karfafa ra'ayin ‘Ba a kankanta a shugabanci .Amma Najeriya na bukatar shugaba kamar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Muna bukatar shi ya jagoranci matasa masu tasowa don ya ba mu damar karbar ragamar shugabancin kasar, ” in ji Kuso.

KU KARANTA: Kungiyar gwamnonin Najeriya sun Allah wadai da harin da aka kai wa gwamnan Benue

A wani labarin daban, Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele, ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya dage da addu’a saboda ya hango rudani a fadar shugaban kasa da ke Abuja, Vanguard News ta ruwaito.

Primate Ayodele ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da mambobinsa a ranar Lahadi kuma lafazin na dauke ne a cikin wata sanarwa da aka tura wa manema labarai.

Ya kuma bayyana cewa jam'iyyar APC, ba za ta sami abubuwa cikin sauki a 2023 ba.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.