Kamfanin MTN ya bai wa Najeriya gudunmawar alluran Korona guda 300,000

Kamfanin MTN ya bai wa Najeriya gudunmawar alluran Korona guda 300,000

- Gwamnatin Najeriya ta karbi gudunmawar allurari 300,000 na rigakafin Korona daga MTN

- Sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya ya tabbatar karbar alluran tare da miki godiya

- Ya kuma kira yi sauran kishiyoyin kamfanoni da su yi koyi da MTN a yaki da cutar Korona

Rundunar Shugaban kasa kan Korona ta ce ta karbi allurai 300,000 na rigakfin Oxford-AstraZeneca daga kamfanin MTN Najeriya, ta ruwaito.

Da yake magana a taron na kasa, Shugaban PTF kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ya ce: “Jiya Lahadi, 21 ga Maris 2021, PTF ta karbi allurai 300,000 na rigakafin Oxford-AstraZeneca daga MTN Najeriya.

"An tabbatar da wannan tare da godiya yayin da muke karfafawa sauran kishiyoyi da su bada gudummawa wajen yakar Korona" in ji Boss Mustpaha.

KU KARANTA: A karkashin mulkin Tinubu ne kadai Najeriya za ta daidaita, in ji wasu manyan arewa

Kamfanin MTN ya bai wa Najeriya gudunmawar alluran Korona guda 300,000
Kamfanin MTN ya bai wa Najeriya gudunmawar alluran Korona guda 300,000 Hoto: thenewsnigeria.com.ng
Asali: UGC

Ku tuna cewa Ministan Lafiya, Dokta Osagie Ehanire, ya ce kashin farko na allurai miliyan 1.4 da aka yi alkawarin bayarwa ga Najeriya zasu iso a karshen watan Fabrairu, yayin da sauran ragowar zasu iso da su a karshen Maris, 2021.

Mista Mustapha ya kuma ce: “Bayyanawar da Masanan na Najeriya suka yi na samar da akalla allurar rigakafin gida biyu ta Korona wadanda ke jiran gwajin asibiti da takaddun shaida na da muhimmanci.

“Wannan wani ci gaba ne abin maraba da zai bude sabon hangen nesa a ci gaban kimiyya kuma zai bunkasa halayya da martabar masana'antar kiwon lafiya a kasar."

KU KARANTA: Akeredolu ga masu son kafa kasar Oduduwa ta Yarbawa: Ku nisanci jiha ta

A wani labarin daban, Gwamnatin Tarayya ta ce za ta roka, maimakon tilasta wa kowa ya yi allurar rigakafin Korona ta Oxford AstraZeneca, a cewar Olorunnibe Mamora, Karamin Ministan Lafiya, Premium Times ta ruwaito.

Mista Mamora ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a, a garin Asaba, yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai jim kadan bayan ya kaddamar da wasu ayyuka a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC) dake Asaba.

Bayanin nasa ya biyo bayan tambayar da wani dan jarida yayi ne kan dalilin da yasa har yanzu jihar Kogi bata karbi rabonta na allurar ba yayin da mafi yawan jihohin tarayya tuni sun karbi nasu kason.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel