Ya kamata Buhari ya dage da addu'a, na hango rudani a nan gaba, in ji wani Fasto

Ya kamata Buhari ya dage da addu'a, na hango rudani a nan gaba, in ji wani Fasto

- Wani malamin coci ya bayyana abubuwan alhini da zasu faru da shugaba Muhammadu Buhari

- Ya bayyana cewa, shugaban na bukatar tsayewa tsayin daka don dagewa da addu'o'i sosai

- Ya hangi abubuwan tsoro da zasu faru da Najeriya, ciki har da tarwatsewar tattalin arzikinta

Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele, ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya dage da addu’a saboda ya hango rudani a fadar shugaban kasa da ke Abuja, Vanguard News ta ruwaito.

Primate Ayodele ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da mambobinsa a ranar Lahadi kuma lafazin na dauke ne a cikin wata sanarwa da aka tura wa manema labarai.

Ya kuma bayyana cewa jam'iyyar APC, ba za ta sami abubuwa cikin sauki a 2023 ba.

KU KARANTA: 'Yan ta'addan Boko Haram sun hallaka sojojin Kamaru a Najeriya

Ya kamata Buhari ya dage da addu'a, na hango rudani a nan gaba, in ji wani Fasto
Ya kamata Buhari ya dage da addu'a, na hango rudani a nan gaba, in ji wani Fasto Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Primate Ayodele ya ce APC ba za ta sami abubuwa cikin sauki ba saboda abubuwan da ke faruwa a fadin kasar.

A cewar Ayodele: ‘‘Najeriya za ta lalace, bashin mu zai karu, kuma wannan zai shafi APC a 2023, ban hango jam’iyyar za ta samu sauki a 2023 ba.

“Abin da na gani mai matukar girma ne, Najeriya ba ta fuskanci komai ba tukunna, tattalin arzikinta zai yi rauni, wannan zai shafi bankuna da kudaden gwamnatin jihohi.

“Mutanen da ke mulkin Najeriya sun batar da kuma barnatar da albarkatunta, akwai wasu abubuwa da za a fallasa a ma'aikatar NNPC.

"Har wa yau, za a kai hari kan jerin gwanon motocin gwamnati, Buhari na bukatar addu'o'i, na ga tsananin rudani a cikin Villa, Yana da matukar muhimmancin da za a bayyana wa duniya."

KU KARANTA: Burutai da sauran hafsoshin tsaro za su bayyana a gaban majalisa kan batun kudin makamai

A wani labarin daban, Gabanin zaben shugaban kasa na 2023, wani tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Yakubu Gowon (mai ritaya), ya yi kira da a raba shugabancin da sauya shi tsakanin shiyyoyin siyasa shida na kasar.

Wannan, in ji shi, zai kasance mafi mahimmanci ga kwanciyar hankali da ci gaban kasar.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Gowon ba yin wannan bayanin ne a wajen bikin cikar kungiyar Tsoffin Dalian Makarantar Barewa (BOBA) shekaru 100 da kafuwa.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel