Kungiyar gwamnonin Najeriya sun Allah wadai da harin da aka kai wa gwamnan Benue

Kungiyar gwamnonin Najeriya sun Allah wadai da harin da aka kai wa gwamnan Benue

- Kungiyar gwamnonin Najeriya sun yi Allah-wadai da harin da aka kaiwa gwamnan Benue

- Hakazalika kungiyar ta siffanta harin aka kaiwa gwamnan da na tsoro ne kum na keta

- Sufeton 'yan sandan Najeriya shima yayi Allah-wadai da harin tare da umartar yin bincike

Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta bayyana harin da 'yan bindiga suka kai wa gwamnan Jihar Benue a matsayin "abin kidimarwa". BBC Hausa ta ruwaito.

A jiya Asabar ne wasu 'yan bindiga suka kai wa tawagar Gwamna Samuel Ortom hari a gidan gonarsa da ke kan hanyar Makurdi zuwa Gboko a jihar ta Benue.

Cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar kuma Gwamnan Jihar Ekiti Kayode Fayemi ya fitar a yau Lahadi, NGF ta taya Ortom alhini game da harin da ta ce "na tsoro ne kum na keta".

KU KARANTA: Ya kamata a samu mataimakan shugaban kasa 2 a Najeriya, Yakubu Gowon

Kungiyar gwamnonin Najeriya sun Allah wadai da harin da aka kai wa gwamnan Benue
Kungiyar gwamnonin Najeriya sun Allah wadai da harin da aka kai wa gwamnan Benue Hoto: punchng.com
Asali: Twitter

Shi ma Sufeto Janar na 'Yan Sanda a Najeriya, Mohammed Adamu ya yi Allah-wadai da harin kuma ya umarci a tsaurara tsaro kan gwamnan tare da kaddamar da bincike cikin gaggawa.

"NGF na fada da babbar murya cewa yunkurin da ake yi na daidaita Jihar Benue ba zai yi nasara ba," a cewar sanarwar.

"A kwanan nan aka kashe daya daga cikin 'yan uwan wani tsohon gwamnan jihar. Wajibi ne a kawo karshen irin wannan aikin na tashin hankali bisa kowane irin dalili domin kashe mazauna Benue."

Legit.ng Hausa a baya ta ruwaito cewa, gwamnan ya bayyana karara cewa, Fulani makiyaya ne suka kai masa harin, lamarin da ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta.

KU KARANTA: Dubban Turawa na zanga-zangar kin amincewa da dokar kulle saboda Korona

A wani labarin da ya gabata, Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan fashi ne sun bude wuta kan ayarin motocin gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa an bude wa ayarin gwamnan wuta ne a ranar Asabar, 20 ga Maris, lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa Makurdi.

Wata jaridar, Daily Trust ta bayyana cewa an yi musayar wuta sosai tsakanin maharan da jami’an tsaron gwamnan.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel