Dubban Turawa na zanga-zangar kin amincewa da dokar kulle saboda Korona

Dubban Turawa na zanga-zangar kin amincewa da dokar kulle saboda Korona

-Dubban Turawa a nahiyar Turai sun shiga zanga-zangar kin amincewa da dokar kullen Korona

- A nahiyar dai ana ganin kara hau-hauwar cutar wanda ya jawo tunanin tsaurara dokar kullen

- 'Yan kasar sun fito zanga-zanga, wanda ya jawo har da jifan 'yan sanda a birnin Landan

Dubban mutane sun shiga zanga-zanga a fadin kasashen Turai don neman a kawo karshen dokokin kulle saboda sake bullowar kwayar cutar Korona.

A garin Kassel na Jamus, 'yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa mutanen da suka taru a kan tituna.

KU KARANTA: Ya kamata a samu mataimakan shugaban kasa 2 a Najeriya, Yakubu Gowon

Dubban Turawa na zanga-zangar kin amincewa da dokar kulle saboda Korona
Dubban Turawa na zanga-zangar kin amincewa da dokar kulle saboda Korona Hoto: itv.com
Asali: UGC

A Hyde Park da ke kasar Landan, an tilasta wa jami'an 'yan sanda gudu zuwa ga motocinsu, yayin da masu zanga-zangar ke jefan su da kwalabe.

Sai dai yawancin kasashen Turai na duba yiwuwar kara tsaurara dokar kullen ne maimakon janye ta saboda samun karuwar masu kamuwa da cutar ta Korona.

Wakilin BBC ya ce mutane da dama a fadin Turai na ci gaba da nuna damuwa a kan jan kafa wajen yin rigakafin Korona a nahiyar, har ta kai ga abin na neman fin karfin gwamnatocin wasu kasashen.

KU KARANTA: Gwamnati ta ce ba za ta tilastawa 'yan Najeriya yin rigakafin Korona ba

A wani labarin daban, Hukumomi a Pakistan sun ce gwaji ya tabbatar da Firaministan kasar Imran Khan ya kamu da korona – kwana biyu kenan bayan ya yi allurar rigakafin ta korona. Yanzu haka ya killace kansa a gida, BBC Hausa ta ruwaito.

Mista Khan wanda yanzu shekarunsa 68 ya halarci wani taron jama’a a kwanakin da suka gabata.

Yawan masu kamuwa da korona na karuwa a Pakistan yayin da cutar ta sake yin kamari karo na uku.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.