Yanzu Yanzu: An yi barin wuta yayinda yan bindiga suka far ma ayarin motocin wani gwamna

Yanzu Yanzu: An yi barin wuta yayinda yan bindiga suka far ma ayarin motocin wani gwamna

-Yan bindiga sun kai wa ayarin motocin Gwamnan Jihar Binuwai, Samuel Ortom, harin kwanton bauna

- An tattaro cewa Ortom na a hanyar dawowa daga Gboko lokacin da lamarin ya faru

- Harin ya afku ne a yau Asabar, 20 ga watan Maris yayinda yake kan hanyarsa ta zuwa Makurdi

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan fashi ne sun bude wuta kan ayarin motocin gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa an bude wa ayarin gwamnan wuta ne a ranar Asabar, 20 ga Maris, lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa Makurdi.

KU KARANTA KUMA: Mun zabi yin garkuwa da mutane ne saboda shine hanya mafi sauki na samun kudi, yan bindiga

Yanzu Yanzu: An yi barin wuta yayinda yan bindiga suka far ma ayarin motocin wani gwamna
Yanzu Yanzu: An yi barin wuta yayinda yan bindiga suka far ma ayarin motocin wani gwamna
Asali: Twitter

Wata jaridar, Daily Trust ta bayyana cewa an yi musayar wuta sosai tsakanin maharan da jami’an tsaron gwamnan.

An tattaro cewa Ortom na a hanyar dawowa daga Gboko lokacin da lamarin ya faru.

A wani labarin, Mai martaba Sarkin Birnin Gwari, Alhaji Zubairu Jibril Mai Gwari II, ya yi magana game da harin da aka kai wa ayarin motocinsa.

KU KARANTA KUMA: Tattaunawa da tubabbun 'yan fashi na da tasiri, in ji Gwamna Ganduje

Mai Gwari ya bayyana cewa idan 'yan fashi suna cikin yankinsa saboda gwal da suke da shi ne, toh a bari su neme shi sannan su bar mutane su sarara.

Da yake magana bayan harin, sarkin wanda ya ba da karin haske a kan harin ya ce gwamnan jihar ya gayyace shi zuwa wani taro a Kaduna.

A wani labarin kuma, mun ji cewa an harbe mai taimakawa Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, Alhaji Abba Abbey Gidan Haki, wanda ’yan bindiga suka sace a daren Alhamis a Sokoto. Anyi jana'izar shi a daren Juma'a, The Nation ta ruwaito.

Babban Limamin Masallacin Juma’a na Sheikh Usman dan Fodiyo dake Sokoto, Sheikh Abubakar Shehu Na Liman ne ya jagoranci sallar jana’izar.

Sallar jana’izar ta samu halartar Sanata Wamakko, Ministan Harkokin ’Yan sanda, Alhaji Muhammadu Maigari Dingyadi da shugaban riko na APC na jihar Sokoto,Alhaji Isa Sadiq Achida.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng