Da duminsa: Fulani Makiyaya suka kai min hari, Gwamna Ortom na jihar Benue

Da duminsa: Fulani Makiyaya suka kai min hari, Gwamna Ortom na jihar Benue

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya bayyana cewa wadanda suka kaiwa ayarin motocinsa hari Makiyaya ne, rahoton TVC.

Ya kara da cewa kimanin mutum 15 wadanda suka kai masa harin sun bibiyeshi zuwa bakin rafi lokacin yana tafiya a kasa.

Wannan ya biyo bayan harin da wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan fashi ne suka kai lokacin da suka bude wuta kan ayarin motocin gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa an bude wa ayarin gwamnan wuta ne a ranar Asabar, 20 ga Maris, lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa Makurdi.

An tattaro cewa Ortom na a hanyar dawowa daga Gboko lokacin da lamarin ya faru.

Fulani Makiyaya suka kai min hari, Gwamna Ortom na jihar Benue
Fulani Makiyaya suka kai min hari, Gwamna Ortom na jihar Benue Credit: @tvcnesng
Source: Twitter

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel