Ya kamata a samu mataimakan shugaban kasa 2 a Najeriya, Yakubu Gowon

Ya kamata a samu mataimakan shugaban kasa 2 a Najeriya, Yakubu Gowon

- Janar Yakubu Gowon (mai ritaya) ya bi sahun mahawarar yadda ya kamata a gudanar da zaben 2023

- Tsohon shugaban ya yi kira da a raba shiyya-shiyya da kuma sauya shugabancin a matakin kasa

- Ga jihohi, Gowon ya nemi kujerar gwamna ya zagaya tsakanin yankuna uku na sanatoci a kowace jiha

Gabanin zaben shugaban kasa na 2023, wani tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Yakubu Gowon (mai ritaya), ya yi kira da a raba shugabancin da sauya shi tsakanin shiyyoyin siyasa shida na kasar.

Wannan, in ji shi, zai kasance mafi mahimmanci ga kwanciyar hankali da ci gaban kasar.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Gowon ba yin wannan bayanin ne a wajen bikin cikar kungiyar Tsoffin Dalian Makarantar Barewa (BOBA) shekaru 100 da kafuwa.

KU KARANTA: Bayan yin rigakafin Korona da kwana 2, Firaminista ya kamu da Korona

Ya kamata a samu mataimakan shugaban kasa 2 a Najeriya, Yakubu Gowon
Ya kamata a samu mataimakan shugaban kasa 2 a Najeriya, Yakubu Gowon Hoto: thenationonlineng.net
Source: UGC

A cewar rahoton, ya kuma bayar da shawarar da a samu mataimakan shugaban kasa guda biyu, daya daga yankin da shugaban ya fito sannan dayan kuma a kada mishi kuri'a a zabe shi zuwa karagar mulki yayin zaben shugaban kasa.

Ya kara da cewa: "Har ila yau, a tsakanin jihohi 19 na arewa ya kamata a sauya matsayin shugaban na Najeriya."

Ya bayyana cewa babu wata kabila da ta fi kyau a wajen kasar kamar yadda take a matsayin Najeriya kasa daya dunkulalliya.

Gowon ya kuma ce matsayin gwamna a dukkan jihohin tarayyar ya kamata ya kasance a zagaye tsakanin gundumomi uku na sanatoci a kowace jiha, ya kara da cewa hakan zai taimaka wajen rage nauyi da kuma kukan nuna wariya.

Ya nanata bukatar da ke akwai na kasancewar kasar nan dunkulalliya, yana mai cewa duk wani yunkuri na wargaza ikon ƙananan hukumomi ya kamata a ki shi.

KU KARANTA: Hadari ne babba yin biris da batun Asari Dukubo, Tofa ya gargadi Gwamnatin Buhari

A wani labarin daban, Doyin Okupe, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya nemi afuwa kan wasu maganganun da yayi a kan shugabancin Igbo a 2023.

Okupe, a cikin wani rubutu da ya wallafa a shafin Twitter ranar Asabar, ya ce ta hanyar yarjejjeniyar kasa ne kadai dan kabilar Ibo zai iya zama shugaban kasa a 2023.

Tsohon hadimin ya kara da cewa irin wannan matsaya ba za ta iya fitowa ba har sai babbar yankin arewa ta yafe wa Ibo a kan juyin mulkin 1966 wanda ya kai ga kashe Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit

Online view pixel