Zamu Hukunta Duk Wanda Ke Da Hannu A Rikicin Zaɓen Cike Gurbi, Inji Gwamnan Ekiti
- Gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi, yasha alwashin hukunta duk wanda aka kama yana da hannu da rikicin da ya ɓarke ranar zaɓen cike gurbi a jihar
- Gwamnan yace baiji daɗin abinda ya faru a jihar tasa ba a Ranar Asabar ɗin data wuce ya yin gudanar da zaɓen cike gurbi
- Andai samu tashe-tashen hankula a jihar ta Ekiti wanda har takai ga rasa rayuka.
Gwamnan jihar Ekiti, Dr. Kayode Fayemi, ya yi Allah wadai da tashin hankalin da ya faru har aka dakatar da zaɓen cike gurbi a mazaɓar Ekiti ta gabas 1 na majalisar dokokin jihar.
Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da kashe mutum biyu a rikicin zaɓen da ya faru ranar Asabar, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Hadari ne babba yin biris da batun Asari Dukubo, Tofa ya gargadi Gwamnatin Buhari
Gwamnan jihar Dr. Kayode Fayemi ta hannun mai magana da yawunsa yace baiji daɗin wannan rikicin ba kuma baza'a kyale shi hakanan ba.
A cewar gwamanan: "Na ba rundunar 'yan sanda umarnin gudanar da bincike, su gano waɗan da sukayi musabbabin rikicin, kuma su tabbatar da an hukunta masu laifin dai-dai da abinda suka aikata."
"Gwamnati bazata taɓa gajiyawa ba a kokarinta na ganin ta kare lafiyar al'ummarta da dukiyoyinsu," inji gwamnan.
"Zamu tabbatar da duk wanda yake da hannu akan lamarin an hukunta shi dai-dai da abinda ya aikata," a cewarsa.
KARANTA ANAN: Albishir matasa: Shugaba Buhari zai fara tallafawa matasa don rage radadin Korona
Sai dai, rundunar 'yan sanda ta bayyana cewa wasu da ake zargin 'yan daba ne suka fara tada yamutsin a runfar zaɓe ta bakwai dake yankin Omuo-Ekiti lokacin da mutanen yankin ke gudanar da zaɓen su.
A wani jawabi da hukumar yan sanda ta fitar ta hannun mai magana da yawun hukumar, Sunday Abutu, ya ce:
"Yan sanda na miƙa jajen su ga iyalan waɗan da suka rasa rayukansu da kuma fatan warkewa ga waɗan da aka jikkata dake asibiti."
Daga cikin waɗan da suka rasa rayuwakansu akwai wata 'yar sanda mace da kuma wani ɗan bautar ƙasa (NYSC).
A wani labarin kuma Gwamnati ta ce ba za ta tilastawa 'yan Najeriya yin rigakafin Korona ba
Ministan ya bayyana cewa, gwamnati bata da shirin tilastawa kowa dole sai ya yi allurar.
Bayanin nasa ya biyo bayan tambayar da wani dan jarida yayi ne kan dalilin da yasa har yanzu jihar Kogi bata karbi rabonta na allurar ba yayin da mafi yawan jihohin tarayya tuni sun karbi nasu kason.
Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.
Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.
Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77 .
Asali: Legit.ng