Hadari ne babba yin biris da batun Asari Dukubo, Tofa ya gargadi Gwamnatin Buhari

Hadari ne babba yin biris da batun Asari Dukubo, Tofa ya gargadi Gwamnatin Buhari

- Alhaji Bashir ya gargadi gwamnati kan batun da Asari Dukubo ya yi na kafa gwamnatinsa

- Tofa ya ja hankalin gwamnati da ta daina daukar irin wannan batu na Asari da abin dariya

- Ya kuma tambaya cewa, me zai iya faruwa idan da dan arewa ne yayi irin wannan magana

Wani dattijo dan kasa, Alhaji Bashir Othman Tofa, ya gargadi gwamnatin tarayya da kada ta yi biris da batun Gwamnatin Gargajiya ta Biyafara (BCG) da Alhaji Asari Dokubo, shugaban kungiyar Ceton Jama'ar Neja Delta (NDPSF) ya shelanta.

Alhaji Dokubo, wanda ya bayyana kansa a matsayin shugaban BCG ya kuma ce za a kafa tsarin larduna ga gwamnati; amma gwamnati, ta bakin Ministan Watsa Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ta mayar da martani game da sanarwar inda ya bayyana ta a matsayin

"Wasan kwaikwayo na wauta daga mai zolaya da ke neman a kula shi.’”

KU KARANTA: Bayan yin rigakafin Korona da kwana 2, Firaminista ya kamu da Korona

Hadari ne gare ku yin watsi da batun Dukubo Asari, Tofa ya gargafi Gwamnatin Buhari
Hadari ne gare ku yin watsi da batun Dukubo Asari, Tofa ya gargafi Gwamnatin Buhari Hoto:s.rfi.fr
Asali: UGC

Dangane da wannan batun, Alhaji Tofa, a wata tattaunawa ta musamman da ya yi da Daily Trust a ranar Lahadi, ya ce:

“Alhaji Asari Dokubo za a iya daukar sa a matsayin mai barkwanci ga wadanda ba su da hikima. Idan furucin sa matakin farko ne kawai a wani babban tsari fa? Bai kamata barazanar da ake yi wa kasar nan ta zama abin dariya ba.”

Ya ce yana mamakin shin Gwamnatin Tarayya za ta tsaya a irin wannan matsayin idan da wani daga Arewa ne ya fadi wani yanki na daga abin da Dokubo ya fada.

KU KARANTA: Albishir matasa: Shugaba Buhari zai fara tallafawa matasa don rage radadin Korona

A wani labarin daban, Gwamnatin tarayya ta kwatanta rahoton samar da gwamnatin gargajiya ta Biafra da Asari Dokubo yayi da wasan yara daga mutum mai bukatar jan hankalin jama'a.

A yayin jawabi ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a kan wannan cigaba a Legas ranar Litinin, ministan yada labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed, yace hankalin shugaban kasa ba zai dauku da wannan shirmen ba.

dan Asari Dokubo na son kafa gwamnatin gwaji ne, zai iya yin hakan. Hankalin wannan gwamnatin ba zai dauko da shirmensa ba saboda muna da abubuwan yi.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel