'Yan Najeriya na adawa da kashe sama da $1.5bn don gyaran matatar mai ta Fatakwal

'Yan Najeriya na adawa da kashe sama da $1.5bn don gyaran matatar mai ta Fatakwal

- 'Yan Najeriya sun fara nuna damuwarsu da kudurin gwamnati na gyara wata matatar man Fetur

- Da yawan 'yan Najeriya na ganin aikin a matsayin almubazzaranci da kudaden kasa ne kawai

- Suna ganin gwanda a gina sabuwar matatar man Fetur maimakon gyara tsohuwa mara tabbas

Wasu 'yan Najeriya sun fara bayyana adawarsu da rashin jin dadi ga shirin gwamnatin tarayya na kashe zunzurutun kudi har Dala Biliyan guda da rabi, domin gyara matatar man fetur mafi dadewa a kasar ta Fatakwal da ke jihar Rivers.

Majalisar zartarwa ta kasa ta amince da fitar da wadannan kudade don yin gagarumin aikin a ranar Laraba da ta gabata.

Ita dai wannan matata ta shafe fiye da shekaru 50 tana aiki, kafin fara samun matsala a shekarun baya bayan nan, lamarin da ake ganin ya haifar da gagarumin cikas wajen tace man a cikin gida.

Sai dai yayin da gwamnatin ke cewa akwai bukatar gyara matatar domin bunkasa tace mai, wasu 'yan Najeriya na bayyana ra'ayin cewa almubazzaranci ne a ware kudi masu yawa irin wadannan don gyara matatar mai guda, kuma a haka ma tsohuwa.

KU KARANTA: Albishir matasa: Shugaba Buhari zai fara tallafawa matasa don rage radadin Korona

Wasu 'yan Najeriya na adawa da kashe Dala Biliyan 1 don gyaran matatar mai ta Fatakwal
Wasu 'yan Najeriya na adawa da kashe Dala Biliyan 1 don gyaran matatar mai ta Fatakwal Hoto: glimpse.ng
Asali: UGC

''Duk mai hankali ya san cewa duk abin da aka ce tsohon abu ne to gyaransa sai a hankali, na biyu matatar man nan wani kamfanin Japan ne ya yi shi, amma yanzu an ce 'yan Italiya ne za su yi wannan gyaran, anya za su iya kuwa?

"Na uku an ce za a shafe fiye da watanni 44 ana gyaran, wannan ma wani abu ne dake tayar mana da hankali'' inji Abubakar Idris, wani dan Najeriya da ya bayyanawa BBC ra'ayinsa.

Ya kuma kara da nuna damuwa a kan makudan kudaden da aka ware don yin aikin, wanda a ganinsa da za a yi amfani da su wajen samar da wasu matatun man za a iya samar da danana da yawa.

Ita kuwa Janet, cewa ta yi da kashe wadannan kudade gwara ma a ce wata sabuwar matatar man za'a yi.

''A tunanina wannan gyara kashe kudi ne, ba lallai bane ma ya yiwu, sannan samun kayan da za a yi amfani da su ma wata wahalace ta daban, don haka a sake tunani'' in ji ta.

Shi kuwa Isiyaku daga jihar Zamfara a Najeriya damuwa ya nuna a kan yadda aka sha fitar da kudi irin wadannan don yin wani aiki a baya, amma sai a rasa inda aka yi da su sama ko kasa.

''Ya kamata a ji tsoron Allah, a kamanta gaskiya, idan ma an cire kudin a cire makimanta ba irin wadannan ba, kuma ai ance kudin za su iya gina wata matatar man, toh ina amfanin cire kudin da za a iya yin sabon abu don gyara tsoho?'' a ra'ayin Malam Isiyaku.

An dai shafe fiye da shekaru 20 ana kokarin gyara wannan matatar man fetur, amma hakan bai yiwu ba, dalilin kenan da wasu ke ganin cewa ba lallai ne a wannan karon ma ya kasance an yi gyaran ba.

KU KARANTA: Bayan yin rigakafin Korona da kwana 2, Firaminista ya kamu da Korona

A wani labarin daban, Wani dattijo dan kasa, Alhaji Bashir Othman Tofa, ya gargadi gwamnatin tarayya da kada ta yi biris da batun Gwamnatin Gargajiya ta Biyafara (BCG) da Alhaji Asari Dokubo, shugaban kungiyar Ceton Jama'ar Neja Delta (NDPSF) ya shelanta.

Alhaji Dokubo, wanda ya bayyana kansa a matsayin shugaban BCG ya kuma ce za a kafa tsarin larduna ga gwamnati; amma gwamnati, ta bakin Ministan Watsa Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ta mayar da martani game da sanarwar inda ya bayyana ta a matsayin:

"Wasan kwaikwayo na wauta daga mai zolaya da ke neman a kula shi.’”

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel