Yanzu Yanzu: Kotu ta tsare Shugaban PDP mai shekaru 80 a Oyo kan kisan kai

Yanzu Yanzu: Kotu ta tsare Shugaban PDP mai shekaru 80 a Oyo kan kisan kai

- An gurfanar da jigon jam'iyyar PDP a Igangan mai suna Pa Olawuwo a gaban kotu kan kisan Dokta Fatai Aborode

- Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar Oyo, Mista Olugbenga Fadeyi ya tabbatar da lamarin inda yace yana nan tsare a hannun yan sanda

- Majiyoyi sun bayyana cewa an hana magoya bayansa ganinsa a lokacin da suka ziyarce shi

An gurfanar da wani jigon jam’iyyar Peoples Democratic Party dan shekaru 80 a Igangan, mai suna Pa Olawuwo a gaban kotu kan kisan Dokta Fatai Aborode.

Jaridar Punch ta tattaro cewa an kama Olawuwo sannan kuma aka kai shi sashen binciken manyan laifuka na Iyaganku a Ibadan.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Najeriya ta samu tallafin biliyan N338 don habbaka kiwon lafiya

Yanzu Yanzu: Kotu ta tsare Shugaban PDP mai shekaru 80 a Oyo kan kisan kai
Yanzu Yanzu: Kotu ta tsare Shugaban PDP mai shekaru 80 a Oyo kan kisan kai Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda a jihar Oyo, Mista Olugbenga Fadeyi, ya shaida wa wakilin jaridar a ranar Juma’a cewa an gurfanar da wanda ake zargin kuma kotu ta tsare shi a hannun‘ yan sanda.

Ya fadi hakan ne a cikin raddi game da tambayar da kafar labaran ta aika masa.

Kakakin yan sandan ya ce, "Eh, an gurfanar da shi a kotu kuma an tura shi hannun 'yan sanda."

Majiyoyi sun shaida cewa dan siyasan da Aborode sun fito daga mazaba daya kuma wasu mabiyansa da suka je inda aka tsare shi ba su samu damar ganinsa.

KU KARANTA KUMA: Yawan yaran da basa zuwa makaranta ya karu da miliyan 3 cikin watanni uku

A wani labari na daban, Michael Wetkas, wani shaidar hukumar yaki da rashawa ta EFCC, ya yi zargi tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido da karbar cin hanci daga hannun yan kwangila da ake bawa aiki a lokacin mulkinsa, rahoton The Cable.

A shekarar 2015, hukumar EFCC ta kama tsohon gwamnan tare da yaransa biyu, Aminu da Mustapha kan zargin almundahar kudade da rashawa.

Daga baya an gurfanar da su a wata kotun tarayya da ke Abuja.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: