Tattaunawa da tubabbun 'yan fashi na da tasiri, in ji Gwamna Ganduje

Tattaunawa da tubabbun 'yan fashi na da tasiri, in ji Gwamna Ganduje

- Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya goyi bayan amfani da karfi da kuma tattaunawa da tubabbun yan fashi

- Ganduje ya ce zama a tattaunar na da muhimmanci mutanen da aka yi garkuwa 'yan uwansu za su so ayi hakan don tsiratar da yan uwan nasu

- Ya kuma ce tattaunawa da tubabbun yan fashin ya iya zama mizani wajen daidaitawa idan aka sace wasu

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya nuna goyon bayansa a kan amfani da karfi da kuma tattaunawa da 'yan fashin daji da ke kisa da garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

Ganduje ya jaddada cewa zama a tattauna da tubabbun 'yan fashi na da muhimmanci musamman ga mutanen da aka yi garkuwa 'yan uwansu.

KU KARANTA KUMA: Mun zabi yin garkuwa da mutane ne saboda shine hanya mafi sauki na samun kudi, yan bindiga

Tattaunawa da tubabbun 'yan fashi na da tasiri, in ji Gwamna Ganduje
Tattaunawa da tubabbun 'yan fashi na da tasiri, in ji Gwamna Ganduje Hoto: Channels TV
Asali: UGC

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata hira da sashin Hausa na BBC, a ranar Juma’a, 19 ga watan Maris.

Game da matsayinsa kan tattaunawa da mayakan Ganduje ya ce:

"Ni a matsayina duka guda biyun na yarda da su, ya danganta da irin matsayin da aka samu, babu shakka ai masu satar mutane da bindiga don a basu kudi babu yadda za a yi ka ce ba za a yake su ba.

"Ai dole ne a yake su a kamo su kamar yadda muke yi mu a jihar Kano wajen satar mutane.

"Amma kuma idan an kai wani yanayi na cewa ga wadansu sun riga sun tuba kuma an yarda sun tuba, kuma yan uwansu wadanda suke wannan aiki na ta’addanci, su za su iya zama gada idan an riga an saci wasu mutane.

"Ina ganin wadanda aka yi musu garkuwa da 'yan uwa za su so a tattauna da masu garkuwar domin sakin yan uwan nasu. Za su so a yi duk abin da za a iya yi domin tsiratar da su. To idan ba ka tattauna da su ba kuma suka kashe su duka fa?

KU KARANTA KUMA: Wajabcin bayyana dukiyoyin ma’aikatan Banki: Sabon Shugaban EFCC ya yi daidai, Barista AlBashir Likko

A wani labarin kuma, wani shugaban ‘yan bindiga a jihar Zamfara, Shehu Rekeb, ya ce kungiyar sa ta haramta ayyukan hakar ma’adanai a duk wuraren da su ke aiki.

Gwamnatin Tarayya ta alakanta ayyukan masu hakar ma'adanai da 'yan bindiga, kuma ta ba da umarnin dakatar da hakar ma'adanai a jihar.

Amma a zantawarsa da Daily Trust, Rekeb ya ce tun kafin umarnin na gwamnatin tarayya, kungiyar tasa ba ta barin masu hakar ma’adanai a wuraren da suke da karfi.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng