Ina son karin yara, Allah zai wadata ni - Yar arewa wacce ta haifi yara 17
- Wata ‘yar Najeriya mai suna Jummai Ibrahim Tsafe, ta ce tana matukar farin ciki da haihuwar 'ya’ya da yawa
- Matar wacce ta rasa bakwai daga cikin yaran da ta haifa ta ce ‘ya’ya ni’ima ne daga Allah kamar yadda Shi ke kula da su duka
- Jummai ta bayyana cewa a shirye take don samun karin yara kuma ba ta damu da abin da tattalin arzikin zai iya hifarwa ba
Wata 'yar Najeriya, Jummai Ibrahim Tsafe, daga jihar Kano, wacce ta haifi' ya'ya 17 ta ce ba ta damu ba idan har za ta samu karin yara 10.
A wata hira da BBC News Pidgin, matar mai shekaru 47 ta ce haihuwar yara kan zo mata da sauki, inda ta kara da cewa guda daya ne kawai ya zo ta hanyar tiyata.
KU KARANT KUMA: Sarkin Birnin Gwari ya bayyana abun da yasa yan bindiga suka kai wa tawagarsa hari
Duk cikin haihuwar da ta yi, sau biyu kawai Jummai ta je asibiti don haihuwa. Sauran duk a gida ta haife su. Matar ta bayyana cewa bakwai daga cikin yaran sun mutu, inda ya sauran mata maza 5 da mata 5.
Matar wacce ta yi aure tana da shekara 14 ta bayyana cewa mutane basa yarda a duk lokacin da ta fada musu yawan yaran da ta haifa.
Jummai ta ci gaba da cewa mutanen da galibi ke tsoron samun yara da yawa ba su san tarin albarkar da ke tattare da yara ba.
Matar ta kara da cewa a shirye take ta kara samun 'ya'ya ba tare da la'akari da karfin tattalin arzikinta ba, tana mai bayyana cewa Allah ne mai bayarwa.
KU KARANTA KUMA: Majalisar Malaman Musulunci ta Najeriya Ta bukaci Ganduje Ya dage Takunkumin da Ya Sakawa Sheikh Abduljabbar
Kalli cikakken bidiyon a kasa:
A wani labari na daban, mun ji wasu 'yan bindiga sun kashe wani matashi lokacin da suka kai hari a gidan mahifinsa a garin Kawo, Jihar Jigawa, yankin Arewa maso yammacin ƙasar nan.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Jihar ta Jigawa, Zahraddeen Aminuddeen, ya tabbatar da faruwar lamarin ga Channels TV.
Ya bayyana wanda lamarin ya faru akansa da suna Sabo Yusuf, ya ce an kai hari gidan mahifinsa da sanyin safiyar Laraba.
Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.
Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.
Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.
Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411
Asali: Legit.ng