Sarkin Birnin Gwari ya bayyana abun da yasa yan bindiga suka kai wa tawagarsa hari

Sarkin Birnin Gwari ya bayyana abun da yasa yan bindiga suka kai wa tawagarsa hari

- Alhaji Zubairu Jibril Mai Gwari II, Sarkin Birnin Gwari ya yi tsokaci a kan harin da wasu yan bindiga suka kai wa tawagarsa

- Sarkin ya bayyana cewa duba ga inda maharan suka karkatar da akalar ta'asarsa, sun yi niyyar kashe shi ne

- Ya kuma yi zargin cewa akwai hadin bakin mutanen garin a harin da aka kai masa

Sarkin Birnin Gwari Alhaji Zubairu Jibril Mai Gwari II ya yi martani a kan harin da wasu yan bindiga suka kai wa ayarin motocinsa a ranar Talata.

A cewar Mai Gwari II, yan bindigar sun yi niyyar raba shi da ransa ne.

Sarkin ba ya cikin ayarin nasa, wadanda suke kan hanyar zuwa birnin Kaduna domin yin taro da gwamnan jihar, lokacin da maharan suka kai musu hari.

Sarkin Birnin Gwari ya bayyana abun da yasa yan bindiga suka kai wa tawagarsa hari
Sarkin Birnin Gwari ya bayyana abun da yasa yan bindiga suka kai wa tawagarsa hari Hoto: BBC.com
Source: UGC

KU KARANTA KUMA: Gwamnan Najeriya ya bayyana dalilin da zai sa ya sauka daga kujerar mulki

A hirar da ya yi da sashin BBC, sarkin ya ce shi aka yi nufin farmawa amma aka samu akasi.

Ya kara da cewa yana zatton akwai hadin bakin wasu mutane da ke garin a wajen kai wa tawagarsa hari.

Ya ce: "Akwai kyakkyawan zato cewa maharan ba za su yi wannan abu ba sai da taimakon wasu. Ka ga idan ka dubi motata, ai ka ga sun yi niyya ne su yi kisan kai, domin ka dubi gilas din gaba sun yi ratata da shi.

"Daidai wurin da na zauna, an fasa gilas din da harsashin bindiga. Hakan na nufin sun yi niyyar su kashe mu ne. Irin wannan kuma ba ka fid da zaton cewa akwai wasu suna nan a cikin gari duk abin da ake yi suna gaya musu."

Mai Gwari II ya ce an yi sa'a ba a samu asarar rai ba, kawai fargaba ce irin ta dan adam da dole sai da suka sha magani daga baya suka samu sukuni.

KU KARANTA KUMA: Majalisar Malaman Musulunci ta Najeriya Ta bukaci Ganduje Ya dage Takunkumin da Ya Sakawa Sheikh Abduljabbar

A baya mun ji cewa, wasu tsagerun yan bindiga sun budewa tawagar motocin Sarkin Birnin Gwari, Alhaji Zubairu Jibril Mai Gwari II, wuta.

Daily Trust ta ruwaito cewa an kai wa motocin sarkin hari ne a hanyar Kaduna zuwa Birnin-Gwari da yammacin ranar Talata.

Za ku tuna cewa gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya gana da Sarakunan gargajiyan jihar ranar Talata.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Source: Legit Newspaper

Online view pixel