'Yan sanda sun sheke 'yan bindiga, sun kwato bindigogi da mota a Kaduna
- Rundunar 'yan sanda a jihar Kaduna ta bayyana hallaka wasu 'yan bindiga garin Saminaka
- 'Yan sandan sun kuma kwato bindigogi da tarin alburusai daga hannun 'yan bindigan a yankin
- Hakazalika, sun kwato wata mota kirar Golf 3 tare da fatattakar 'yan bindiga zuwa cikin daji
Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce mutanenta sun kashe wasu 'yan bindiga biyu a Saminaka na karamar hukumar Lere ta jihar.
Rundunar ta kuma bayyana cewa abubuwan da aka kwato daga samamen sun hada da; bindigogin AK47 guda biyar, bindiga kirar G3 guda daya, tarin gidan alburusai guda 17 da kuma mota kirar Golf.
Kakakin rundunar, ASP Mohammed Jalige ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, yana mai cewa, wasu ‘yan bindiga da yawa sun tsere zuwa cikin daji sun bar makaman su na aikata barna.
KU KARANTA: Tsoho mai shekaru 80 ya koka a kotu kan matarsa mai hana shi jima'i
A cewar ASP Jalige, rundunar ta samu bayanan sirri daga majiya mai tushe, in da ya bayyana cewa:
“A ranar 17 ga watan Maris 2021, da misalin karfe 10: 45 na safe, hadaddiyar kungiyar FIB, STS, TIU da Operation Yaki na rundunar a yayin da suke aiki da sahihan bayanan sirri, sun bi wasu da ake zargin 'yan bindiga ne zuwa garin Saminaka na karamar hukumar Lere.
“Amma, 'yan bindigan wadanda ke dauke da muggan makamai da suka hango isowar jami’an 'yan sanda nan da nan suka fara harbin kan mai uwa da wabi ta bangarori daban daban.
"Wannan ya haifar da mummunar musayar wuta tsakanin su da jami'an 'yan sanda wanda karfin wutar da kuma karfin aikin na 'yan sanda ya yi nasarar kawar da 'yan bindigan biyu tare da raunata wasu da dama da suka tsere cikin daji suka bar makamansu na barna.
Ya bayyana nasarar da rundunar ta samu saboda kwarin gwiwa da dabaru da suka nuna ya haifar da kwato:
Bindigogin AK-47 guda biyar, bindiga G-3 daya, gidan albursai na AK-47 guda 17, tarin alburusai 1,658 masu zagayen 7.62 x 39mm naAK-47 da kuma motar kirar Golf 3 daya.”
KU KARANTA: Ina da ciki wata 4, dan haka na gudu da saurayina, budurwa ta ajiye wa iyayenta wasika
A wani labarin, Rundunar sojojin Najeriya ta ce ta samu nasarar kashe wasu 'yan ta'addan Boko Haram a yankin Dikwa a jihar Borno, BBC Hausa ta ruwaito.
Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin rundunar Mohammed Yerima wanda ya fitar a ranar Laraba, ya ce rundunar ta samu wannan nasara ne tare da hadin gwiwar wasu 'yan sintiri a yammacin ranar Litinin.
Cikin bata kashin da aka yi karkashin atisayen "TURA TAKAIBANGO", an samu nasarar kashe 'yan ta'addan na Boko Haram 6 tare da kwato wasu makamai masu yawa.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng