Tsoho mai shekaru 80 ya koka a kotu kan matarsa mai hana shi jima'i

Tsoho mai shekaru 80 ya koka a kotu kan matarsa mai hana shi jima'i

- Wani tsohon malamin jami'a ya koka a gaban kotu kan batun matarsa mai hanashi hakkinsa

- Malamin ya bukaci kotu da ta tilastawa matarsa amincewa dashi a gadon aurensu kasancewar bata yarda

- Sai dai, matar ta yi alwashin hana shi hakkinsa saboda aikata lalata da yake yi da wasu matan amininsa

Wani tsohon malamin jami'a mai ritaya dan shekaru 80, Farfesa Muritala Haroon, a ranar Alhamis ya fada wa Kotun Al’adu da ke zaune a Mapo, cewa matarsa, Afsat, har yanzu ta ki amincewa da shi, Daily Nigerian ta ruwaito.

A lokacin da aka ci gaba da sauraran karar, Mista Haroon ya ce: “Matata ba ta bi shawarar da wannan kotu ta ba ta ba don samar da damar zaman lafiya ya ci gaba ta hanyar amincewa da aiwatar da aikinta na matar aure.

Sai dai, Afsat ba ta halarci zaman kotun ba lokacin da aka kira ta kuma babu wanda ya wakilce ta a kotun.

Shugaban kotun, Cif Ademola Odunade, ya gargadi Haroon da ya kara hakuri.

KU KARANTA: Ina da ciki wata 4, dan haka na gudu da saurayina, budurwa ta ajiye wa iyayenta wasika

Tsoho mai shekaru 80 ya koka a kotu kan matarsa mai hana shi jima'i
Tsoho mai shekaru 80 ya koka a kotu kan matarsa mai hana shi jima'i Hoto: geraldrogers.com
Asali: UGC

“Kotu za ta yi aiki tare da danginta don warware matsalar cikin ruwan sanyi,” inji shi.

Mista Odunade ya daga karar zuwa ranar 17 ga watan Mayu don ci gaba da sauraran karar.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ba da rahoton cewa Haroon a watan Fabrairu ya nemi a raba aurensa mai tsawon shekaru 52 saboda kuntata masa kan hakkinsa na aure da kuma barazana ga rayuwarsa.

A cikin karar, ya yi zargin cewa Afsat na matukar son korarsa a makwanci tare da garkame kofa.

”Ba zan kuma iya jure irin wannan halin ba. Mafi munin har yanzu, ita da danginta suna son ganin baya na.

“Afsat tayi yunkurin soka min wuka. Tana lalata yaranmu guda shida. Ta juya musu tunani zuwa hantarata,” in ji shi.

Afsat a cikin amsarta, ta ki amincewa da bukatar rabuwa.

”Farfesa yana aikata lalata. Ba zan iya yin komai da shi ba saboda ya kwanta da matan amininsa har mata uku.

"Maigidana, Haroon ya kwanta da matan uku na mutumin da ke tsayawa a matsayin mai shiga tsakani a duk lokacin da muke da matsala," in ji ta.

KU KARANTA: Matsalarmu ba shugabancin 2023 bane, adalci muke so a yiwa mutane, Makinde

A wani labarin daban, Inyang Ekwo, Alkali mai shari’a a babban kotun tarayya da ke garin Abuja, ya gargadi hukumar EFCC a wajen shari’ar da ake yi da Sanata Shehu Sani.

Jaridar Premium Times ta ce Alkali Inyang Ekwo ya gargadi EFCC ne a kan jirkitar da hujjoji a shari’ar da ake yi da tsohon Sanatan Kaduna, Shehu Sani.

Alkali mai shari’a ya yi wannan kashedi ne bayan da lauyan wanda ake zargi, Abdul Ibrahim SAN, ya koka kan wani bayani da EFCC ta yi a shafinta na Twitter.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel