Sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka gungun 'yan Boko Haram a Borno
- Rundunar sojojin Najeriya a jihar Borno sun samu nasarar hallaka 'yan Boko Haram da dama
- A wani samame da sojojin suka kai, sun kashe tare da kwato wasu kayayyaki a hannun 'yan ta'addan
- Daga cikin abinda aka kwato, an samu motoci da bindigogi kirar AK-47 da sauran makamai
Rundunar sojojin Najeriya ta ce ta samu nasarar kashe wasu 'yan ta'addan Boko Haram a yankin Dikwa a jihar Borno, BBC Hausa ta ruwaito.
Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin rundunar Mohammed Yerima wanda ya fitar a ranar Laraba, ya ce rundunar ta samu wannan nasara ne tare da hadin gwiwar wasu 'yan sintiri a yammacin ranar Litinin.
KU KARANTA: Abdurrasheed Bawa ya bukaci ma'aikatan banki da su gaggauta bayyana kadarorinsu
Cikin bata kashin da aka yi karkashin atisayen "TURA TAKAIBANGO", an samu nasarar kashe 'yan ta'addan na Boko Haram 6 tare da kwato wasu makamai masu yawa.
Sanarwar ta ce an samu nasarar kwato motoci biyu da bindigogin kirar AK 47 da sauran wasu nau'ukan makamai masu hadari a yayin harin.
A wani makamancin irin wannan samamen da aka kai an samu nasarar kwato wayar salula biyu, wadanda a yanzu ake gudanar da bincike kansu.
KU KARANTA: El-Rufai: Aikina shine tilasta doka ba yiwa 'yan bindiga wa'azin su tuba ba
A wani labarin daban, Adadi mai yawa na rundunar 'yan ta'addan Boko Haram da na takwarorinsu ISWAP sun yi kicibus da rundunar sojojin Operation Lafiya Dole a yankin Tafkin Chadi da Tumbus.
Rahoto ya tabbatar da cewa, rundunar sojin sun kashe adadi mai yawa na 'yan ta'addan kungiyar ta Boko Haram da ISWAP.
Hadakar sojojin na sashin da ke sintiri a kan iyakar Tafkin Chadi sun ci gaba tare da share kauyukan Daban Massara da Ali Sherifti da sauran kauyukan da 'yan ta'addan suka mamaye, kafin daga bisani suka wuce gaba.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng