Ina da ciki wata 4, dan haka na gudu da saurayina, budurwa ta ajiye wa iyayenta wasika

Ina da ciki wata 4, dan haka na gudu da saurayina, budurwa ta ajiye wa iyayenta wasika

- Wani mahaifi ya tsinci wata wasika mai taba zuciya da diyarsa 'yar shekara 16 ta rubuta

- Yarinyar ta bayyana cewa, tana da ciki wata uku kuma ta fece da saurayinta domin cin soyayyarsu

- Sai dai, a karshen wasikar, komai ya sauya yayin da yarinyar ta bayyana wasu kamlamai masu cike da hikima

Wani mahaifi ya tsinci wasika mafi ban mamaki a rayuwarsa daga diyarsa 'yar shekara 16.

A cewar TopRadio, abinda ya faru shine, kungiyar wasan da mutumin ya fi so ta yi rashin nasara a wani wasa, lamarin da ya dagula masa lissafi har ya shiga dakin diyarsa domin ya dauke ta su je su sha Ice-Cream.

Abin ya ba shi mamaki, da ya samu wata rubutacciyar takarda a kan gadonta, The Real Journal ta ruwaito.

KU KARANTA: Rikici ya barke a majalisar dattawan Najeriya kan batun matsalar tsaro

Ina da ciki wata 4, dan haka na gudu da saurayina, budurwa ta ajiye iyayenta wasika
Ina da ciki wata 4, dan haka na gudu da saurayina, budurwa ta ajiye iyayenta wasika Hoto: therealjournal.com
Asali: UGC

"Zuwa ga Mama da Baba,

"Ku yi hakuri da abinda zan gaya muku, amma zan tsallaka tare da sabon saurayina Muhammad.

"A karshe na sami soyayya ta gaskiya, kuma kyakkyawa ne! Ina son musamman madaukakiyar hujinsa, zane mai kyau a jikinsa, da kuma babbar babur dinsa!

"Kuma ba wannan kadai ba - Ina tsammanin yaro tare da Muhammad, kuma tuni na sami ciki wata uku. Za mu zauna a cikin gidansa, kuma ya ce yana son yara da yawa.

"Ina murna sosai!!! Kuma kun san wani abu? Za mu yi aure mako mai zuwa!

"Ya kuma bayyana min cewa wiwi tana da kyau ba kamar yadda wasu mutane ke fadi ba, don haka yanzu zamu shuka tsirrai 17 a bayan gidansa. Zai wadatar da shi da abokansa, su kuma sakamakon haka 'Zasu bamu kwayoyi iya yadda muke so.

"Ina fatan cewa likitoci su sami maganin cutarsa ba da dadewa ba domin Muhammad ya sami sauki - yana bukatar hakan.

"Kada ku damu da batun kudi - Abokan Muhammad Juan da Stanislav suna harkar kasuwancin fim, kuma sun shirya yadda zasu mayar dani 'yar fim!

"Aikin yana biya da kyau, dala 50 a kowane dauka, kuma zan sake samun wasu 50 idan akwai maza sama da uku a wuri daya. Don haka kada ku damu da ni - Ni 'yar shekara 16 ne kuma zan iya kula da kaina.

KU KARANTA: Rikici ya barke a majalisar dattawan Najeriya kan batun matsalar tsaro

"Nan gaba kadan idan nazo ziyara, za ku ga jikanku!

" Xoxo, Anna."

Kamar dai yadda wasikar ta kasance mai taba zuciya, ta kare da cewa:

"Ka sani Baba, babu zance daya da yake gaskiya a wasikar nan - kawai na tsallaka zuwa wurin Emma ne don kallon talabijin.

"Ina so in tunatar da kai cewa akwai abubuwa masu muni a rayuwa fiye da kungiyar The Patriots tasha kashi a hannun The Eagles!

"Gani nan zuwa nan ba dadewa ba!"

KU KARANTA: Matsalarmu ba shugabancin 2023 bane, adalci muke so a yiwa mutane, Makinde

A wani labarin daban, Rundunar 'yan sanda ta jihar Kano ta ce ba a yi garkuwa da amaryar da za a aurar ba, Amina Gwani Danzarga tun da farko kamar yadda iyayenta da jama'a suka yi imani.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda a jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya shaida wa Daily Trust cewa budurwar ta buya ne saboda ba ta son auren.

Ya ce budurwar ta shirya duk yadda aka yi tunanin ta bace, hakan ya sa iyayenta da mai neman ta suka yi imanin cewa an sace ta 'yan sa'o'i kadan zuwa shirin daurin auren nata.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel