Rundunar sojoji ta yi kicibus da 'yan Boko Haram, an yi rashin sojoji 3

Rundunar sojoji ta yi kicibus da 'yan Boko Haram, an yi rashin sojoji 3

- Rundunar sojin Najeriya sun samu nasarar fatattaka tare da kashe 'yan ta'adda a Borno

- Rundunar ta yi kicibus da 'yan ta'addan Boko/ISWAP a wani yanki kusa da Munguno

- Sai dai, rundunar ta yi asarar wani jami'i tare da wasu jaruman soja uku a yayin harin

Adadi mai yawa na rundunar 'yan ta'addan Boko Haram da na takwarorinsu ISWAP sun yi kicibus da rundunar sojojin Operation Lafiya Dole a yankin Tafkin Chadi da Tumbus.

Rahoto ya tabbatar da cewa, rundunar sojin sun kashe adadi mai yawa na 'yan ta'addan kungiyar ta Boko Haram da ISWAP.

Hadakar sojojin na sashin da ke sintiri a kan iyakar Tafkin Chadi sun ci gaba tare da share kauyukan Daban Massara da Ali Sherifti da sauran kauyukan da 'yan ta'addan suka mamaye, kafin daga bisani suka wuce gaba.

KU KARANTA: 'Yan Najeriyan da suka tare a kasashen waje basu da ta cewa kan matsalar kasar

Rundunar sojoji ta yi kicibus da 'yan Boko Haram, an yi rashin sojoji 3
Rundunar sojoji ta yi kicibus da 'yan Boko Haram, an yi rashin sojoji 3 Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Bayan tafiyar akalla kilomita 14 daga sansaninsu, tsakanin Kukawa da Munguno, sun hangi motocin bindiga daga Boko Haram/ISWAP, tuni suka afkawa 'yan ta'addan inda suka kashe da dama.

Sai dai jami'i daya daga cikin rundunar sojin da sojoji uku sun mutu yayin da wasu da dama suka jikkata a harin.

Wata sanarwa da ta fito daga ofishin jami'in hulda da jama'a na rundunar, Birgediya Janar Mohammed Yerima, ta ce: "an kashe 'yan ta'adda da dama tare da lalata motocinsu na bindiga.

"Amma abin takaici, jami'i 1 da jaruman soji 3 sun rasa rayukansu yayin da wadanda suka ji rauni a halin yanzu ke karbar kulawar likita a asibitin rundunar soji ta 7 dake sansanin Maimalari."

KU KARANTA: Wasu jami'o'in Kotono 8 da dalibansu ba a amince su yi bautar kasa ba (NYSC)

A wani labarin, Shugaban 'yan ta'addan Boko Haram, Abubakar Shekau, ya caccaki malamin addinin Islama da ke zaune a Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, saboda tattaunawa da 'yan bindiga.

Kwanan nan Gumi ya shiga rangadi zuwa maboyar ‘yan bindigan dake dauke da muggan makamai a dazuka domin kulla yarjejeniyar zaman lafiya da masu tada kayar bayan.

Zagayen malamin ya jawo maganganu daban-daban a tsakanin ‘yan Nijeriya, inda mutane da yawa, ciki har da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai, suka yi Allah wadai da matakin.

Amma a cikin wani faifan murya da ya kai tsawon awa 1 da mintuna 55, wanda aka samo daga jaridar Daily Nigerian, Shekau ya ce Gumi na daga cikin wadanda suke yin barna da ganganci.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel