Atiku ya sake jan hankalin gwamnatin Buhari biyo bayan sace dalibai a Kaduna

Atiku ya sake jan hankalin gwamnatin Buhari biyo bayan sace dalibai a Kaduna

- Atiku Abubakar ya sake shawartar gwamnatin tarayya kan matsalar sace daliban makaranta

- A baya ya shawarci gwamnati da cewa, ta gaggauta sanya dokar ta baci a wasu makarantun

- Hakazalika ya sake jaddada shawararsa da cewa, bai kamata a bari lamarin satar ta ci gaba ba

A ci gaba da sace-sacen daliban makarantu a arewacin Najeriya, fitattun 'yan Najeriya na ta bada shawarwari kan hanyoyin da ya kamata a bi a magance matsalar tsaro.

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, kuma dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP a zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar ya nuna rashin jin dadinsa da hare-haren.

Biyo bayan harin safiyar ranar Litinin a wata makarantar firamare dake wani yankin Birnin Gwari, Atiku ya bayyana wani mataki da yake ganin ya kamata gwamnatin tarayya ta dauka a fannin ilimi a kasar.

A cewarsa, ya kamata kwamnati ta dauki matakin sanya dokar ta baci a fannin ilimi saboda ci gaba da hare-haren tare da girke sojoji a bakin wasu makarantun.

KU KARANTA: Indiya za ta bi sahun Najeriya a harmata Bitcoin tare da garkame masu shi

Atiku ya sake jan hankalin gwamnatin tarayya biyo bayan sace dalibai a Kaduna
Atiku ya sake jan hankalin gwamnatin tarayya biyo bayan sace dalibai a Kaduna Hoto: Council on Foreign Relation
Asali: UGC

@atiku ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa: "Tare da sabon sace daliban Kaduna, ina maimaita kira ga FG da ta ayyana dokar ta baci a bangaren ilimi kuma ta sanya masu gadi dauke da makamai kowane lokaci a kowace makaranta a jihohin da abin ya shafa da makwabtan jihohi.

"Babu wani kudi da za ayi asara don kiyaye makarantunmu lafiya.

"Tare da yara miliyan 13.5, Najeriya tuni ta zama hedkwatar duniya ta yaran basa zuwa makaranta.

"Wannan na iya kara dagula lamura. Ya zama wajibi a kanmu a matsayinmu na al'umma mu yi aiki tukuru mu kawar da wannan matsalar na satar 'yan makaranta daga cikinmu tare da ingantattun manufofi da suka dace.

"Dole ne kuma mu daina yawaita biyan kudin fansa. Mafita ne na gajeren lokaci wanda zai haifar da lalacewa na dogon lokaci.

"Dole ne, a matsayinmu na kasa, mu sanya doka da oda a yanzu, ko kuma mu yi wasici da rashin bin doka da hargitsi ga tsararraki masu zuwa. Kuma Allah ya kiyaye hakan."

KU KARANTA: Rundunar sojoji ta yi kicibus da 'yan Boko Haram, an yi rashin sojoji 3

A wani labarin, Wasu daliban makarantar firamare uku da aka sace ‘yan awanni da suka gabata lokacin da wasu 'yan bindiga suka farma makarantar firamaren UBE da ke Rama a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna sun tsere.

Da yake zantawa da daya daga cikin malaman makarantar, Daily Trust ta tattaro cewa tun farko an sace dalibai uku na firamare amma sun tsare lokacin da ‘yan bindigar suka yi kokarin satar wasu shanu da babura a wata unguwa da ke kusa.

Naomi Francis, wata malama a makarantar, wacce ta tsira daga satar, ta tabbatar wa Daily Trust cewa daliban uku sun kubuta amma ta ce 'yan bindigan sun buge su.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel