Aure a muslunce: Mafi karancin sadakin aure ya haura Naira dubu 22 bana

Aure a muslunce: Mafi karancin sadakin aure ya haura Naira dubu 22 bana

- Ba a aure a musulumci sai dole an bada sadaki a matsayin hakkin mace da za a aura

- Mafi karancin sadakin da za a ba mace daga watan Maris din bana ya haura Naira duba 22

- Diyyar rai ya haura miliyan 88 yayin da nisabin Zakkah kuwa, ya kai har sama da N1,767,520

Daya daga cikin sharuddan aure a addinin musulunci shine namiji ya bai wa mace sadaki.

Kudin sadaki mafi kankanta ya kai sama da naira dubu 22 a watan Maris na shekarar 2021.

Duk wata Kwamitin Fadar Sarkin Musulmin Najeriya na fitar da bayani kan nisabin Zakka da sadakin aure da diyyar rai.

Kuma kwamitin ya ce daga ranar 28 ga watan Rajab shekarar 1442 bayan hijira daidai da 12 ga watan Maris na shekarar 2021, nisabin Zakka ya kai N1,767,520, wato adadin kudin da za a fitar wa Zakka kenan.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun sace wasu mutum 11 a Suleja

Aure a muslunce: Mafi karancin sadakin aure ya haura Naira dubu 22 bana
Aure a muslunce: Mafi karancin sadakin aure ya haura Naira dubu 22 bana Hoto: Jefferies Solicitors
Asali: UGC

Kudin sadaki mafi kankanta kuma da haddin sata ya kai N22,094.

Kudin da mutum kuma zai biyya na diyyar musulmi da aka kashe ya kai ga Naira miliyan 88 da dubu 376.

KU KARANTA: Dalilin da ya sa na bada shawarin nada Abdurrasheed Bawa shugaban EFCC, Malami

A wani labarin daban, Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar koli kan Harkokin Addinin Musulunci (NSCIA), Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya ayyana ranar Litinin 15 ga Maris, a matsayin ranar farko ta watan Sha’aban 1442AH, The Guardian ta ruwaito.

Abubakar, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Farfesa Sambo Junaidu, shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin addini, majalisar masarautar ta Sokoto ya fitar.

"Kwamitin Shawara na Majalisar Masarautar Muslunci kan harkokin Addini tare da hadin gwiwar kwamitin kula da watanni na kasa ba su samu wani rahoto da ke tabbatar da ganin jinjirin watan ba."

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel