Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun sace wasu mutum 11 a Suleja

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun sace wasu mutum 11 a Suleja

A ranar Lahadin da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga suka sace mutane 11 a garin Chaza, wani gari da ke wajen garin Suleja a cikin jihar Neja.

Shugaban rundunar ‘yan sanda na yankin Suleja CSP Sani Badarawa ya tabbatar da faruwar lamarin.

Mazauna yankin sun ce 'yan bindigan sun mamaye wasu gidaje ne don yin garkuwa da wadanda suka yi garkuwar da su wadanda a cikinsu akwai wani malami, Malam Abdulfatah.

Wasu na danganta lamarin da dakatar da sintirin jami'an hadin gwiwa na tsaro a yankin.

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun sace wasu mutum 11 a Suleja
Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun sace wasu mutum 11 a Suleja Hoto: RFI
Source: UGC

Source: Legit.ng

Online view pixel