Baku isa ba: Shugaba Buhari ya gargadi 'yan bindigan da ke sace dalibai

Baku isa ba: Shugaba Buhari ya gargadi 'yan bindigan da ke sace dalibai

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kakkausa kashedi ga gungun 'yan bindiga masu sace dalibai

- Ya bayana cewa, bazai bari su lalata harkar karatu da ilimi a kasar ba yana ji yana kallonsu

- Ya kuma yabawa sojoji da irin namijin kokarin da suke yi na kawo zaman lafiya a sassan kasar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kakkausar kashedi ga ‘yan ta’adda da 'yan bindiga da ke addabar makarantu, yana mai cewa kasar ba za ta bari a lalata tsarin makarantu ba, PM News ta ruwaito.

Shugaban ya yi wannan gargadin ne a cikin wata sanarwa daga babban hadiminsa na musamman kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu, a Abuja ranar Asabar.

Buhari ya mayar da martani ne kan mamaye Kwalejin Harkar Noma da Gandun Daji ta Tarayya dake Afaka a jihar Kaduna, da wasu mahara suka yi a ranar Juma’a.

KU KARANTA: Mun biya bokaye da 'yan banga N14m don yaki da 'yan bindiga a wani yankin Neja

Baku isa ba: Shugaba Buhari ya gargadi 'yan bindigan da ke sace dalibai
Baku isa ba: Shugaba Buhari ya gargadi 'yan bindigan da ke sace dalibai Hoto: Daily Nigerian
Source: UGC

Ya yaba da kokarin gwamnatin jihar Kaduna da kuma martanin da sojoji suka yi cikin gaggawa wanda ya kai ga ceto dalibai 180 ciki har da ma’aikata takwas.

Amma, ya yi kira da cewa sauran da aka bayyana sun bata sun a ganosu kuma su dawo ga danginsu lami lafiya.

Shugaban ya kuma yaba da kokari da gudummawar da jama'a ke bayarwa na leken asirin don dakile masu satar mutane.

”Kasar da ke da ingantacciyar hanyar sadarwa ta cikin gida kasa ce mafi aminci.

"Sojojinmu na iya kasancewa masu inganci kuma suna da makamai amma suna bukatar kyakkyawan kokari don kare kasar kuma dole ne jama'ar gari su tashi zuwa yakar kalubalen na wannan lokacin."

Buhari, duk da haka, ya tausaya wa wadanda lamarin Afaka ya rutsa da su kuma ya yi fatan karshen irin wannan tashin tashina.

KU KARANTA: Mun biya bokaye da 'yan banga N14m don yaki da 'yan bindiga a wani yankin Neja

A wani labarin, Wani tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani a ranar Lahadi ya koka kan yadda 'yan bindiga suka zama abin ban tsoro a wajen garin Kaduna.

Ya yi magana ne dangane da yunkurin satan mutane da aka yi kokarin dakilewa a rukunin gidajen ma'aikatan tashar jirgin saman Kaduna da safiyar Lahadi.

Wasu ‘yan bindiga da safiyar Lahadi sun sake yin wani yunkuri na garkuwa da wasu ma’aikatan jirgin sama da ke zaune a rukunin ma’aikata na Hukumar Kula da Jiragen Sama na Tarayyar Najeriya (FAAN) a filin jirgin sama na Kaduna.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit.ng

Online view pixel