Da duminsa: Shugaban EFCC ya bayyana a kotu dan shaida batun zamba kan man fetur

Da duminsa: Shugaban EFCC ya bayyana a kotu dan shaida batun zamba kan man fetur

- Shugaban hukumar EFCC yau ya bayyana a gaban kotu domin bada shaida kan wani batu

- Shugaban ya bada shaida kan zambar da kamfanin Nadabo Energy ya yi biliyoyin kudade

- Kamfanin yayi amfani da takardun jabu domin karbar kudade daga asusun gwamnatin tarayya

Shugaban Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arziki Zagon Kasa (EFCC), Abdulrasheed Bawa, ya bayyana a gaban wata babbar kotu da ke Ikeja don bayar da shaida a shari'ar zamba ta biliyan N1.4 da ta shafi wani kamfanin mai mai suna Nadabo Energy.

Bawa, kafin a tabbatar da shi a matsayin shugaban EFCC, ya bayyana a gaban kotun a bara a matsayin shaidan mai gabatar da kara, Vanguard News ta ruwaito.

Hukumar ta EFCC ta zargi Abubakar Ali Peters da kamfaninsa, Nadabo Energy da zargin yin amfani da takardun jabu don karbar N1,464,961,978.24 daga Gwamnatin Tarayya.

KU KARANTA: Zamu bai wa Kiristocin Arewa mafakar siyasa a Biafra, Nnamdi Kanu

A na zargin kamfanin ne da zambar kudin a matsayin tallafin mai bayan an zarge ta da fadada yawan kudin man fetur da aka ce an ba ta har na miliyan 14,000.

Wadanda ake tuhumar sun musanta laifin da ake tuhumarsu dashi.

Da duminsa: Shugaban EFCC ya bayyana a gaban kotu dan shaida wani batu na zamba man fetur
Da duminsa: Shugaban EFCC ya bayyana a gaban kotu dan shaida wani batu na zamba man fetur Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Bawa, a cikin shaidar da ya gabatar, ya shaida wa kotun cewa bisa binciken da aka gudanar kan hulda da wanda ake kara da Kamfanin Inshora na Staco, "Takaddar inshorar da wanda ake tuhumar ya yi amfani da ita don hada-hadar da ake magana ta jabu ce."

Mai shari’a Balogun ya daga karar zuwa ranar 10, 16, 23 da 9 ga Maris, 2021 don ci gaba da shari’a.

Bawa a yanzu haka yana bayar da karin shaida a shari'ar kamar yadda a lokacin hada wannan rahoton.

KU KARANTA: Wata sabuwa: 'Yan bindiga sun sace mutane sama 55 a jihar Katsina

A wani labarin, Abdulrasheed Bawa, shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), ya ce a karkashin jagorancinsa, hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa za ta himmatu wajen yaki da cin hanci da rashawa, The Cable ta ruwaito.

Shugaba Muhammadu Buhari ne ya nada Bawa a watan Fabrairu kuma daga baya majalisar dattijai ta tabbatar da shi a matsayin shugaban hukumar ta EFCC. Da yake jawabi a ranar Juma'a lokacin da ya hau kujerar a hukumance, Bawa ya yi alkawarin jan ragamar hukumar zuwa ga bin diddigi da binciken sirri.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.