Shehu Sani ya bayyana yadda 'yan bindiga suka kara zama abin tsoro a Kaduna
- Sanata Shehu Sani ya koka kan yadda lamarin rashin tsaro ke kara kamari a yankin Kaduna
- Ya bayyana cewa, 'yan bindiga a yankunan Kaduna na kara zama ababen tsoro ga jama'a
- Ya bukaci hukumomin tsaro da su gaggauta magance irin wadannan matsaloli a yankunan
Wani tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani a ranar Lahadi ya koka kan yadda 'yan bindiga suka zama abin ban tsoro a wajen garin Kaduna.
Ya yi magana ne dangane da yunkurin satan mutane da aka yi kokarin dakilewa a rukunin gidajen ma'aikatan tashar jirgin saman Kaduna da safiyar Lahadi.
Wasu ‘yan bindiga da safiyar Lahadi sun sake yin wani yunkuri na garkuwa da wasu ma’aikatan jirgin sama da ke zaune a rukunin ma’aikata na Hukumar Kula da Jiragen Sama na Tarayyar Najeriya (FAAN) a filin jirgin sama na Kaduna.
KU KARANTA: Wani Kansilan unguwa a jihar Kano ya kaddamar da hadimansa na mulki mutum 18
Wannan na zuwa ne kimanin makonni biyu bayan da wasu 'yan bindiga suka sami nasarar shiga filin jirgin saman kuma suka yi awon gaba da ma'aikata 11.
Sun yi awon gaba da mutanen da suka kunshi ma'aikatan hukumar kula da sararin samaniyar Najeriya (NAMA) da iyalansu da kuma na Hukumar Kula da Yanayin Sama ta NiMET da kuma iyalansu su ma.
@ShehuSani, a shafinsa na Twitter, ya bukaci hukumomi da su tsaurara matakan tsaro a filin jirgin saman domin kariya ga ma'aikatar, da ma'aikatanta da danginsu.
Ya ce: “Ana bukatar taka tsantsan don kare Filin Jirgin Saman, da ma’aikatan sa da iyalan su.
"'Yan fashin sun kara nuna abin tsoro da karfin gwiwa a wajen garin mu."
KU KARANTA: Yanzun nan: An yi bata-kashi tsakanin sojoji da 'yan bindiga a filin jirgin sama na jihar Kaduna
A wani labarin daban, Akalla dalibai 307 aka ceto yayin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari makarantar sakandaren kimiyya ta gwamnati dake Ikara a karamar hukumar Ikara da ke Kaduna a safiyar ranar Lahadi, The Nation ta ruwaito.
Kwamishanan tsaron cikin gida da harkokin cikin gida, Mista Samuel Aruwan, ya tabbatar da faruwar harin.
A cewarsa, "Dalibai 307 ne aka samu nasarar kubutar da su ba tare da wani rauni ba" daga sojojin da suka dakile yunkurin satar.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng