Wani Kansilan unguwa a jihar Kano ya kaddamar da hadimansa na mulki mutum 18

Wani Kansilan unguwa a jihar Kano ya kaddamar da hadimansa na mulki mutum 18

- Wani kansilan wata unguwa a jihar Kano ya yi abinda ake kira da ko da me kazo an fika

- Kansilan ya dauki hadimai sama da mutum 10 domin taimaka masa a gudanar da aikinsa

- Kansilan ya bayyana hakan da yunkurin samar da ji da gani daga wajen talakawa da halin da suke ciki

Wani kansila a jihar Kano ya yi abin da ba a saba gani ba ta hanyar nada mutum 18 wadanda za su yi aiki tare da shi wajen gudanar da ayyukan da aka dora masa.

Kansilan, Hon Muslihu Yusuf Ali, mai wakiltar unguwar Guringawa na karamar hukumar Kumbotso, ya kaddamar da hadiman 18 a sakateriyar karamar hukumar a ranar Alhamis tare da taimakon Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar, Shamsu Abdullahi.

Da yake zantawa da Daily Trust bayan an rantsar da shi, Hon Ali ya ce a kullum burinsa shi ne ya kawo canje-canje idan ya samu dama; damawa da kowa tare da aiki da ci gaban jama'arsa.

Hon Ali ya ce, a matsayinsa na shugaba, akwai bukatar ya nada ko da hadimai sama da 18 ne domin su taimaka masa da kuma bayar da rahoton abin da mutane suke bukata daga tushe wanda a cewarsa, shugabanni da yawa ba sa damuwa da yi.

KU KARANTA: Ba zan bari 'yan ta'adda su lalata mana tsarin ilimi ba, in ji shugaba Buhari

Wani Kansilan unguwa a jihar Kano ya kaddamar da hadimansa na mulki mutum 18
Wani Kansilan unguwa a jihar Kano ya kaddamar da hadimansa na mulki mutum 18 Hoto: News Flash 247
Asali: UGC

Ya bayyana cewa, “Wannan yana daya daga cikin tsare-tsare na, kuma na dade ina addu’a ga hakan.

"Idan ka lura da kyau, tsarin wakilci tun daga Majalisar kasa har zuwa majalisun jihohi, ba a bai wa ‘yan majalisa damar nada wadatattun hadimai da za su tallafa musu a aikinsu ba - kuma su ne wadanda suka fi kusa da talakawa.

"Hakanan a matakin ƙananan hukumomi, muna haɗuwa da talakawa a ƙasa kuma muna shaida abin da suke ciki.

"Abin da ya sa na yanke shawarar fito da wannan canjin kenan. Na nada hadimai a kan kowane bangare na ci gaba kuma ina fatan yin aiki tare da su wajen bunkasa al'ummarmu.

Dangane da hanyar da yabi wajen zaban hadiman nasa, Ali yace: “Na zabi mutane ne wadanda suke aiki tukuru kuma suke iya gudanar da ayyukansu daban-daban.

"Na bi ka'idoji uku wajen yin hakan. Na lura cewa a siyasa mutanen da kuka fara samun matsala da su sune wadanda suka ba ku goyon baya a lokacin yakin neman zabe.

"Don haka na zabi wasu daga cikinsu don cike wannan tazarar. Na zabi wasu daga cikin mutanen da ba su ma shiga kamfen dinmu ba, amma sun cancanci hakan saboda ina wakiltarsu duka.

"Ina so in tabbatar muku da cewa wasun su kawai sun gani a wasiku cewa an nada su ne kuma sun yarda da hakan.”

A kan hanyoyin da zai bijiro da kudi don biyan hadiman, kansilan ya ce siyasa ba ko yaushe ta kebanta da kudi ba, akwai batun ci gaban mutane da jama’arsu, ya kara da cewa dan kanslila bawan mutane ne kuma yana siyasa ba don kudi ba, sai don kawo ci gaba mai kyau.

KU KARANTA: Da duminsa: An kashe mutum 1, an yi won gaba da mutum 6 a wani yankin jihar Neja

A wani labarin, Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Sojoji, Sanata Ali Ndume, ya ce zai saba wa kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC ace arewa ta samar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar na gaba, Daily Trust ta ruwaito.

Dan majalisar, wanda ke wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattijai, ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da kungiyar Correspondents' Chapel, kungiyar 'yan jaridu ta Najeriya da Majalisar Tarayya ta shirya a ranar Asabar.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel