Da duminsa: Jami'an tsaro sun sake dakile harin 'yan bindiga na yunkurin sace dalibai 307 a Kaduna

Da duminsa: Jami'an tsaro sun sake dakile harin 'yan bindiga na yunkurin sace dalibai 307 a Kaduna

- Jami'an tsaro da suka hada da soji dan 'yan sanda sun samu nasarar kubutar da wasu dalibai

- A yau ne da safiyar ranar Lahadi 'yan bindiga suka kai hari makarantar GSSSS Ikara a Kaduna

- Jami'an tsaron sun fatattaki 'yan bindiga tare da murkushe yunkurinsu na sace daliban makarantar

Akalla dalibai 307 aka ceto yayin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari makarantar sakandaren kimiyya ta gwamnati dake Ikara a karamar hukumar Ikara da ke Kaduna a safiyar ranar Lahadi, The Nation ta ruwaito.

Kwamishanan tsaron cikin gida da harkokin cikin gida, Mista Samuel Aruwan, ya tabbatar da faruwar harin.

A cewarsa, "Dalibai 307 ne aka samu nasarar kubutar da su ba tare da wani rauni ba" daga sojojin da suka dakile yunkurin satar.

KU KARANTA: Wani Kansilan unguwa a jihar Kano ya kaddamar da hadimansa na mulki mutum 18

Da duminsa: Jami'an tsaro sun sake dakile harin 'yan bindiga na yunkurin sace dalibai 307 a Kaduna
Da duminsa: Jami'an tsaro sun sake dakile harin 'yan bindiga na yunkurin sace dalibai 307 a Kaduna Hoto: The Nation
Asali: UGC

Aruwan ya ce: “Tsakanin tsakiyar daren ranar Asabar zuwa wayewar garin yau, wasu da ake zargin’ yan bindiga ne sun mamaye makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati ta Ikara, da ke karamar hukumar Ikara, a kokarin sace daliban.

“Abin farin cikin shi ne, daliban sun yi amfani da tsarin gargadi na tsaro da aka tanada don haka suka samu damar sanar da jami’an tsaro a yankin.

"Jami'an tsaron da suka hada da sojojin na Najeriya, 'yan sanda da kuma wasu jami'an sa kai na tsaro sun hanzarta zuwa makarantar inda suka yi artabu da 'yan ta'addan, suka tilasta su suka tsere."

KU KARANTA: Hukumar NAFDAC ta kusa kammala gwajin magungunan gargajiya don magance Korona

A wani labrin daban, Rundunar soji ta sake dakile wani yunkuri da wasu ‘yan bindiga dauke da makami suka yi na sace ma’aikatan jirgin sama da ke zaune a rukunin ma’aikata na hukumar kula da filayen jiragen saman Najeriya (FAAN) a filin jirgin saman Kaduna.

Wannan na zuwa ne kusan makonni biyun makamancin wannan yunƙurin tare da yin garkuwa da wasu ma'aikata 13 ciki har da ma'aikatan Hukumar NAMA da danginsa da na Hukumar NIMET lokacin da 'yan ta'addan suka kai hari a baya.

Yunkurin da aka yi na baya-bayan nan wanda ya afku a safiyar ranar Lahadi ya jawo artabu tsakanin 'yan bindigan da sojoji wadanda suka kutsa cikin filin jirgin don ceton wadanda abin ya shafa.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.