Kwadago zata fara zanga-zangar baji-ba-gani kan batun mafi karancin albashi

Kwadago zata fara zanga-zangar baji-ba-gani kan batun mafi karancin albashi

- Kungiyar kwadago ta Najeriya ta bayyana shiga zanga-zangar nuna rashin jin dadi kan batun mafi karancin albashi

- Kungiyar ta siffanta majalisar wakilai da zama mai son kai da kokarin lalata aikin 'yan Najeriya

- Kungiyar ta bukaci mambobinta da su fito domin nuna rashin jin dadinsu, musamman ga majalisar

Kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) da kawayenta, a ranar Laraba, za su fara zanga-zanga a duk fadin kasar kan matakin da Majalisar Dokoki ta Kasa ta dauka na cire mafi karancin albashi daga jerin dokoki na musamman zuwa jerin dokokin majalisar.

Takardar gayyata a hukumance da Majalisar ta aike wa kungiyar kwadago ta bayyana cewa tattara mambobin zai fara ne daga Unity Fountain Abuja da karfe 7:30 na safe, kuma za su tafi farfajiyar Majalisar Dokoki ta kasa don nuna bacin ransu kan matakin.

Shugaban NLC, Ayuba Wabba, a makon da ya gabata, ya ce za a gudanar da zanga-zangar a majalisun dokoki na jihohi 36 na Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: Yanzun nan: Gwamna Dapo Abiodun ya zama gwamna na farko da ya fara yin rigakafin Korona

Kwadago zata fara zanga-zangar baji-ba-gani kan batun mafi karancin albashi
Kwadago zata fara zanga-zangar baji-ba-gani kan batun mafi karancin albashi Hoto: Iya Kao
Asali: UGC

Ya bayyana manufar yin zanga-zangar da mayar da martani ga shirin da Majalisar Wakilai ta yi na sauya tsarin albashin na yanzu, wanda ya ba Gwamnatin Tarayya ikon tattauna mafi karancin albashi ga ma'aikata a kasar.

Wabba, wanda ya sake bayyana abubuwan da mambobin suka gabatar bayan wani taron gaggawa na Majalisar Zartarwa ta Kasa a Abuja, ya sha alwashin cewa NLC zata yi tir da "duk wani yunkuri na wargaza rukunin ma'aikata na Najeriya."

Shugaban ya bayyana cewa ma’aikatan ba za su kalli “hakkokin gwagwarmayarsu wadanda suke matsayin mizanin duniya da 'yan siyasan da suka samu dama kuma masu karamin tunani suke barnatar da su ba”

Ya kara da cewa kudirin wani yunkuri ne na lalata ma’aikatan Najeriya.

Majalisar Wakilai, makonni biyu da suka gabata, ta yi muhawara kan kudirin cire ikon sasanta batun albashi daga jerin dokoki na musamman zuwa jerin dokokin majalisar, tare da nuna gazawar gwamnonin jihohi na iya biyan N30,000 mafi karancin albashi.

Amma shugaban NLC ya ce: “NEC ta yanke shawarar cewa za a gudanar da zanga-zangar kasa wanda zai fara daga 10 ga Maris, 2021, a Babban Birnin Tarayya da kuma musamman ga Majalisar Dokoki ta Kasa.

“Hukumar NEC ta yanke shawarar cewa idan bukatar hakan ta taso, ta baiwa majalisar gudanarwa ta kasa ta NLC ikon ayyanawa tare da aiwatar da yajin aiki a kasar.

Hukumar ta kuma bayyana cewa ba batun ja da baya matukar "'yan majalisar suka ci gaba a kan tafarkin lalatawa na matsar da mafi karancin albashin kasa daga jerin dokoki na musamman zuwa jerin dokokin majalisar a lokaci daya.”

KU KARANTA: Babu wanda zai tsira sai kowa yayi rigakafin Korona, in ji Boss Mustapha

A wani labarin daban, Shararren marubuci Farfesa Wole Soyinka, a ranar Asabar ya ce daga yanzu, duk jihar da ake satar yara ya kamata ta rufe don nuna rashin amincewa da ta'addancin, The Punch ta ruwaito.

Soyinka ya kuma shawarci sauran jihohin da ke makwabtaka, a matsayin hadin kai, su ma su shiga zanga-zangar tare da rufe jihohinsu.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.