Mijin Zahra Buhari ya nuna hotunansa tare da zakin da yake wasa dashi a gida, ya jawo cece-kuce
- Daya daga cikin sirikan shugaba Buhari ya fidda wasu hotunan abin mamaki a gidansa
- Sirikin nasa, mijin Zahra Buhari, ya fidda hotunan wata dabba da ya kira da dabbarsa ta wasa
- Sai dai wasu a kafafen sada zumunta suna ganin dabbar mai hadari ce da bai kamata ya rike ba
Ahmed Indimi, sirikin Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), ya watsa hotunan wani farin zaki a shafukan sada zumunta tare da taken “sabuwar dabba ta.”
Ya bayyana a fili a wannan zamani, rayuwa tare da dabbobi masu hadari ya zama ruwan dare ga mutane musamman fitattun 'yan Najeriya idan aka yi la’akari da yadda wasunsu suka dauki dabbobin daji a matsayin dabbobin gida.
A wani sabon rubutu a shafin Instagram, Indimi wanda ya kasance suruki ne ga Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, ya watsa hotunan farin zakin yayin da yake rike da shi daure da igiya.
KU KARANTA: An kama gurbatattun kwayoyin magani na biliyan 6 a Jihar Kano
Indimi ya raka hotunan tare da rubutu mai sauki inda ya bayyana cewa farin zakin shine sabon dabbarsa ya kuma bayyana cewa yana son dabbar. Yayi jin karfin gwiwa yayin da yake rike da dabbar.
KU KARANTA: Yanzun nan: An yi bata-kashi tsakanin sojoji da 'yan bindiga a filin jirgin sama na jihar Kaduna
A cikin sashen tsokaci, wani @amma_licious ya ce, "Ina fata dai wasa ne saboda wadannan dabbobi ne masu hadari. Yawan su yana raguwa saboda farauta da irin wadannan ayyukan na kebe su kamar dabbobin gida."
Myrablac: "*Yanzu wasan Egungun kake, sai ka kiyaye ko kuma ka tafi cikin sauki*"
Amounalemouna: "Dubi yadda tsoro ya cika idanun ka. Tazarar da kake bayarwa ma tukuna."
Wata Lilvicky68 a majallar Nairaland ta ce, "Ina fatan zakin ya dan bashi cizon soyayya."
Wani memban mujallar mai suna Wallade, ya ce, “A cikin kasa mai hankali, Hukumar Kula da Dabbobi ko Kungiyar Kare Hakkin Dabbobi ne za ta dauki dabbar daga inda take tsare, da yardarsa ko ba tare da izininsa ba.
"Babu wanda ke da hakkin kiyaye dabba mai hadari kamar zaki a matsayin dabbar gida. Dabbar na gidan kallon dabbobi ne ko na daji.”
A wani labarin, Wani kansila a jihar Kano ya yi abin da ba a saba gani ba ta hanyar nada mutum 18 wadanda za su yi aiki tare da shi wajen gudanar da ayyukan da aka dora masa.
Kansilan, Hon Muslihu Yusuf Ali, mai wakiltar unguwar Guringawa na karamar hukumar Kumbotso, ya kaddamar da hadiman 18 a sakateriyar karamar hukumar a ranar Alhamis tare da taimakon Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar, Shamsu Abdullahi.
Da yake zantawa da Daily Trust bayan an rantsar da shi, Hon Ali ya ce a kullum burinsa shi ne ya kawo canje-canje idan ya samu dama; damawa da kowa tare da aiki da ci gaban jama'arsa.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng