Sojoji sun dakile yunkurin sace daliban makarantar Turkish dake Kaduna

Sojoji sun dakile yunkurin sace daliban makarantar Turkish dake Kaduna

- Sojojin Najeriya a jihar Kaduna sun yi bajintar dakile harin 'yan bindiga a wata makaranta

- Sojojin sun sami nasarar fatattakar 'yan bindigar yayin da suka hanasu daukar dalibi ko daya

- Hakazalika sun samu nasarar kwato wasu daga cikin daliban da aka sace a safiyar yau Juma'a

Sojojin rundunar gaggawa ta 1 na rundunar Sojin Najeriya sun dakile wani yunkuri da wasu 'yan bindiga suka yi don sace daliban makarantar Sakandaren Kasa da Kasa ta Turkiyya da ke Rigachikun, Jihar Kaduna, in ji Sojojin, The Nation ta ruwaito.

Daraktan hulda da jama'a na rundunar Birgediya Janar Mohammed Yerima, a cikin wata sanarwa, ya yi bayanin: “Yin aiki da wata shawara kan abin da ke gabatowa na sace daliban makarantar, sojoji da sauri suka hada kai don kare makarantar daga‘ yan bindiga.

KU KARANTA: Da duminsa: Dimeji Bankole ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC

Sojoji sun dakile yunkurin sace daliban makarantar Turkish dake Kaduna
Sojoji sun dakile yunkurin sace daliban makarantar Turkish dake Kaduna Hoto: The Guardian Nigeria
Asali: UGC

“Duk da haka, a yayin da sojojin ke kokarin kare makarantar sakandaren, wani kiran na daban ya zo cewa 'yan bindigar sun mamaye Makarantar Harkokin Noma da Gandun daji ta Tarayya, Afaka, karamar Hukumar Igabi da ke jihar da nufin yin garkuwa da ma’aikata da daliban.

"Sojojin sun hanzarta zuwa Afaka inda suka dauki matakin shawo kan 'yan ta'addan."

Ya kara da cewa: “Bayan musayar wuta, sojoji sun sami nasarar ceto mutane 180, wadanda suka hada da dalibai maza 132, dalibai mata 40 da kuma ma’aikatan farar hula mutum 8.

“An ce 'yan bindigan sun kutsa kai cikin makarantar ne ta hanyar keta shingen makarantar.

“An kwashe daliban da aka kubutar zuwa wani wuri mai aminci yayin da wadanda suka jikkata a yanzu haka suke karbar kulawar likita a wani sansanin soji.

"A halin yanzu hadaddiyar rundunar sojojin sama, 'yan sanda da DSS a halin yanzu suna zagaye a dajin don neman 'yan bindigan".

KU KARANTA: Tuna baya: Buhari yace an yi na karshe daga kan daliban Jangebe, sai kuma ga na Kaduna

A wani labarin, An samu rudani lokacin da jami'an runduna ta 7 ta sojojin Najeriya dake Maiduguri, suka gano kakin sojoji da katunan shaidar sojoji 145 da aka sauya a garin Marte da ke jihar Borno.

Lamarin ya faru ne ‘yan awanni kadan bayan da aka binne sojoji bakwai da aka kashe a wata arangama da suka yi da masu tayar da kayar baya a ranar 14 ga Fabrairu, 2021

A yayin harin, rahotanni sun ce maharan sun kona kayayyakin soji, da suka hada da motoci, tare da sace babura da kayayyakin abinci.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.