Da duminsa: An kashe mutum 1, an yi won gaba da mutum 6 a wani yankin jihar Neja

Da duminsa: An kashe mutum 1, an yi won gaba da mutum 6 a wani yankin jihar Neja

- Ana ci gaba da sace-sacen mutane a wasu sassan arewacin Najeriya, daya daga ciki; jihar Neja

- An hallaka mutum daya, tare da yin awon gaba da wasu mutane shida a kauyen Erena dake Shiroro

- Majiya ta bayyana cewa, sama da 'yan bindiga 50 ne suka kai hari garin dauke da muggan makamai

'Yan bindiga sun kashe mutum daya tare da yin garkuwa da wasu mutum shida a yankin Erena da ke karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja.

Wannan shine hari na biyu da al'ummomin yankin ke gani cikin kasa da makonni biyu a jihar.

KU KARANTA: Bayan yin allurar Korona, gwamnan Bauchi ya roki Buhari ya nemo kudin siyan kari

Yanzu-yanzu: An kashe mutum 1, an yi won gaba da mutum 6 a wani yankin jihar Neja
Yanzu-yanzu: An kashe mutum 1, an yi won gaba da mutum 6 a wani yankin jihar Neja Hoto: Daily Trust
Source: Facebook

'Yan bindigar sun kai harin ne cikin tsakar dare dauke da muggan makamai.

Wasu majiyoyi sun fadawa jaridar The Nation cewa ‘Yan bindigar sun fi 50 kuma sun kara da cewa wasu mutanen da dama sun samu rauni a kokarinsu na tserewa daga sace su.

A wani labarin daban, Wasu ‘yan bindiga dauke da muggan makamai, a safiyar ranar Alhamis, sun kashe wani jami’in 'yan sanda tare da kona gidaje da dama ciki har da ofishin ‘yan sanda a yankin Tse Harga da ke karamar hukumar Katsina-Ala a jihar Benue.

An tattaro cewa yan bindigan da ake zargin yara ne ga babban mai kisan gilla, Terwase Akwaza wanda aka fi sani da 'Gana', sun afkawa yankunan karkara da misalin karfe 4:00 na asuba sannan suka fara harbin kan mai uwa da wabi.

An bayyana cewa, sun kone gidaje da dama tare da bankawa wani ofishi da motar 'yan sanda wuta.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit.ng

Online view pixel