An kashe matar tsohon kwamishinan ‘yan sanda a jihar Benue

An kashe matar tsohon kwamishinan ‘yan sanda a jihar Benue

- Wasu mahara da ba asan ko su waye ba sun hallaka matar wani tsohon kwamishinan 'yan sanda

- Tsohon kwamishinan ya taba rike zama kwamishina a jihar Benue kafin daga bisai a ka mai dashi Kogi

- Rundunar 'yan sandan jihar Benue ta tabbatar da faruwar lamarin, kuma ana ci gaba da bincike

An kashe Eunice Aghanya, matar tsohon kwamishinan ‘yan sanda, Ibezimako Aghanya mai ritaya na jihar Benue.

Aghanya ya taba zama kwamishinan ‘yan sanda a Benue kafin a sauya shi zuwa Kogi inda ya yi ritaya shekaru da yawa da suka gabata.

Daily Trust ta rahoto cewa an kashe Eunice ne a ranar Juma’a a gidanta da ke kusa da David Mark Bye-Pass a Makurdi, babban birnin jihar Benue.

KU KARANTA: Da duminsa: An kashe mutum 1, an yi won gaba da mutum 6 a wani yankin jihar Neja

An kashe matar tsohon kwamishinan ‘yan sanda a jihar Benue
An kashe matar tsohon kwamishinan ‘yan sanda a jihar Benue Hoto: The Nation
Asali: UGC

Marigayiyar ta yi amannar cewa maharan sun bi ta gida saboda rahotanni sun ce ta koma gidanta da misalin karfe 4:00 na yamma tare da ajiye motarta a wajen kofar shiga.

An gano cewa marigayiyar ta rayu a gidan ne ita kadai.

Mijinta, Aghanya, wanda ke zaune a Legas, yana zargin cewa wani abu ya faru, ya kira kaninsa a Makurdi don ya duba masa matar tasa a daren Juma’a.

Wani ganau ya shaida wa manema labarai cewa, “A lokacin da kanin Aghanya ya isa wurin sai da ya fasa ƙofar shiga gidan saboda ya ga motarta tana tsaye a waje.

"Da shigarsa, ya ga Mama Aghanya a kwance cikin jininta wanda tuni ta mutu. Maharanta sun yayyanka ta a kai da yawa.”

Lokacin da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sanda ta Benue, DSP Catherine Anene, ta ce, “An tabbatar da faruwar lamarin. Ana ci gaba da bincike kuma bayanai za su same ku nan ba da dadewa ba don Allah.”

KU KARANTA: Shugabannin hafsun soji sun sake dira jihar Borno don fatattakar Boko Haram

A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa don kare tsarin makarantun kasar nan daga 'yan bindiga, masu satar mutane da 'yan ta'adda da ke kokarin rusa ta, The Nation ta ruwaito.

Shugaban ya yi magana game da matsalolin da ke faruwa a kwanan nan na masu satar mutane da hare-haren 'yan bindiga a makarantu da sace daruruwan yara 'yan makaranta.

Shugaban ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da Babban Mataimakinsa na Musamman kan Harkokin Yada Labarai da Yada Labarai, Malam Garba Shehu ya fitar.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.