Kwana uku a jere 'yan bindiga na kai hari kauyen 'Yar Nasarawar-Akubu a Zamfara

Kwana uku a jere 'yan bindiga na kai hari kauyen 'Yar Nasarawar-Akubu a Zamfara

- Al'umomin wani yankin jihar Zamfara sun shiga halin ha'ula'i a wannan makon saboda hare-hare

- Kwanaki uku mutanen yankin 'Yar Nasarawar-Akubu suka yi ana kai musu munanan hare-hare

- 'Yan bindigan sun kashe mutane, sannan sun sace amfanin gona tare da fatattakar mutanen garin

Daruruwan mutanen 'Yar Nasarawar-Akubu na karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara, suna can suna zaman gudun hijira a makwabtan garuruwa, cikin mawuyacin hali.

Sun fuskanci kalubalen jerin hare-hare har uku da 'yan bindiga suka kai musu tun daga ranar Talata har zuwa jiya Alhamis.

Wani mutumin garin da ya bukaci a sakaya sunansa ya bayyana wa BBC cewa a halin yanzu babu kowa a garinsu kuma shi ma yana magana ne daga mafakarsa.

"Mutane ne ke taimaka mana da abinci tunda a halin yanzu a gidan wasu muke a zaune. Da mu da matanmu da 'ya'yanmu.A takure muke, wasu daga cikinmu ma a shago aka dan raba mu muke kwana," a cewarsa.

A cewarsa, ranar Talata bayan sun idar da sallar la'asar ne 'yan bindigar suka shiga garinsu tafe a kan babura kusan su 40 suna barin wuta da bindigogi.

KU KARANTA: Sojoji sun dakile yunkurin sace daliban makarantar Turkish dake Kaduna

Kwana uku a jere 'yan bindiga na kai hari kauyen 'Yar Nasarawar-Akubu a Zamfara
Gwamna jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle | Hoto: Vanguard News
Source: UGC

"A haka suka kashe mutum 12 sannan wadanda suka tsere ma suka bi su daji suka rika harbinsu."

Ya ce bayan sun gama kashe mutane kuma sun dibi amfanin gona da sauran kayan abinci suka tafi da su.

"Sai maghariba suka bar garin amma washegari da safiyar ranar Laraba sun sake dawowa a lokacin da muke kokarin yin jana'izar mutanen da suka kashe a daren Talata," kamar yadda ya shaida.

Ya ce a nan ma sai tserewa mutane suka yi suka bar gawarwakin da ake shirin yi wa sallah. Ya ce maharan ba su kashe kowa ba ranar Laraba amma sun kwahsi kayan abinci kuma sun balla shaguna sun yi sata.

Ya ce jami'an tsaro sun isa garin ne da la'asar suka ba mutanen gari kariya har suka yi wa 'yan uwansu jana'iza.

Mutumin ya ce jami'an tsaron ba su tsaya sun ba mutanen garin kariya ba don ana gama jana'izar suka tafi kuma maharan sun sake dawowa ranar Alhamis da safe inda suka tarar da 'yan tsirarun mutane da suka je tattara sauran amfanin gonarsu.

Jihar Zamfara na daya daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fama da matsalar tsaro musamman 'yan bindiga masu satar mutane da barayin daji.

KU KARANTA: Da duminsa: Dimeji Bankole ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC

A wani labarin daban, A ranar Juma’a, ‘yan Najeriya suka farka da labarin sake sace daliban da wasu 'yan bindiga suka yi - hari na uku mafi girma da aka kaiwa makarantu a shekarar 2021.

Daily Trust ta ruwaito yadda wasu ’yan bindiga suka afka wa Kwalejin Harkar Noma da Gandun Daji ta Tarayya da ke yankin Mando a Jihar Kaduna suka yi awon gaba da wasu daliban da ba a san adadinsu ba.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit

Online view pixel