Da duminsa: Dimeji Bankole ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC
- Tsohon kakakin majalisar wakilai ta kasa Bankole ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC
- Tsohon kakakin ya gana da shugaban jam'iyyar ta APC tare wasu masu ruwa da tsaki a Abuja
- Tsohuwar jam'iyyarsa ta nuna rashin jin dadinta dangane da sauya shekarsa zuwa jam'iyyar APC
Tsohon kakakin majalisar wakilai kuma dan takarar Gwamnan Ogun a jam'iyyar ADP na 2019, Dimeji Bankole ya koma jam’iyya mai ci ta APC.
Ya gana da shugaban jam'iyyar APC, Kwamitin Kula da na Shirye-shiryen Babban Taron (CECPC), Gwamna Mai Mala Buni a Abuja tare da rakiyar Gwamnan Jigawa Abubakar Bagudu.
Ganawar, wacce ta gudana a gidan shugaban jam’iyyar APC da ke Abuja, ta dauki kusan tsawon awa guda.
Kokarin da aka yi don samun ko da daya ne daga cikin shugabannin suyi magana ya ci tura yayin da taron ya zama na sirri amma sun dauki hotuna.
KU KARANTA: Gwamna Zulum ya dauki nauyin karatun 'ya'yan talakawa, 'yan mata 800
Amma wata gajeriyar sanarwa daga Malam Mamman Mohammed, Darakta Janar na Harkokin Labarai ga Gwamna Buni, ta tabbatar da taron.
Ya ce: “Shugabannin uku sun tattauna kan batutuwa da dama na siyasa da suka hada da shigar tsohon Shugaban majalisar da magoya bayansa zuwa cikin jam’iyyar.
"A bayyane yake cewa damar APC a jihar Ogun na ci gaba da fadada."
Dangane da ci gaban, Shugaban jam'iyyar ADP na kasa, Engr. Yabagi Sani, ya fada wa The Nation cewa jam’iyyarsu ba ta ji dadin matakin da Bankole ya dauka ba.
Sani ya ce: “Wannan dan siyasan Najeriya ne a gare ku. Ba su yi imani da ginawa ba sai dai rabawa. Na yi tunani duba da shekarunsa da gogewarsa, zai nuna kyakkyawan misali. Matakin da ya dauka ya fi bakanta rai amma ba mu karaya ba."
KU KARANTA: Tuna baya: Buhari yace an yi na karshe daga kan daliban Jangebe, sai kuma ga na Kaduna
A wani labarin, Jam’iyyar PDP ta bayyana kwarin gwiwar karbar mulki daga hannun jam’iyyar APC mai mulki a shekarar 2023.
Sakataren yada labaran ta na kasa, Kola Ologbondiyan, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise wanda The Nation ta nakalto.
Ya ce: “A shiyya daya daga cikin shida, muna da dan takarar mulkin da ke haifar da rashin jituwa wanda tuni kwamitin sulhu karkashin jagorancin Sanata Bukola Saraki ta sasanta.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng