Tuna baya: Buhari yace an yi na karshe daga kan daliban Jangebe, sai kuma ga na Kaduna

Tuna baya: Buhari yace an yi na karshe daga kan daliban Jangebe, sai kuma ga na Kaduna

- Biyo bayan sace daliban Jangebe a jihar Zamfara, shugaba Buhari ya yi ikrarin cewa satan shine na karshe

- Sai dai, a yau Juma'a aka tashi da mummunan labarin sace dalibai a jihar Kaduna, arewacin Najeriya

- Sace daliban a Kaduna ya biyo bayan ikirarin Buhari da kuma jibge jami'an tsaro a jihar Zamfara

A ranar Juma’a, ‘yan Najeriya suka farka da labarin sake sace daliban da wasu 'yan bindiga suka yi - hari na uku mafi girma da aka kaiwa makarantu a shekarar 2021.

Daily Trust ta ruwaito yadda wasu ’yan bindiga suka afka wa Kwalejin Harkar Noma da Gandun Daji ta Tarayya da ke yankin Mando a Jihar Kaduna suka yi awon gaba da wasu daliban da ba a san adadinsu ba.

Wannan ya faru ne makonni biyu bayan gwamnatin da Shugaba Muhammadu Buhari ke jagoranta ta yi alkawarin cewa kasar ba za ta sake ganin makamancin wannan ba bayan sace 'yan Makarantar Sakandaren ’Yan Mata ta Gwamnati, da ke Jangebe, a Jihar Zamfara.

KU KARANTA: Gwamna Zulum ya dauki nauyin karatun 'ya'yan talakawa, 'yan mata 800

Tuna baya: Buhari yace an yi na karshe daga kan daliban Jangebe, sai kuma ga na Kaduna
Tuna baya: Buhari yace an yi na karshe daga kan daliban Jangebe, sai kuma ga na Kaduna Hoto: Check Point Charley
Asali: UGC

A watan Fabrairu ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari makarantar da ke karamar hukumar Talata-Mafara a Zamfara inda suka yi awon gaba da dalibai sama da 200.

Wannan ya zo ne makonni bayan an sace dalibai da ma’aikatan Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati dake Kagara, Jihar Neja wadanda daga bisani aka sake su.

Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, wanda ya jagoranci wata tawaga ta shugaban kasa zuwa Zamfara, ya ce abin da ya faru a Jangebe zai zama na karshen kai hari kan makarantu da sace dalibai a Najeriya.

"Wannan satar daliban mata a Jangebe zai zama na karshe saboda Gwamnatin Tarayya ta sake fasalin jagororin tsaron kasar don gano duk irin ta'asar da wadannan masu laifi ke yi," in ji shi.

"Shugaban kasar ya yi bakin ciki da sace daliban daga Jangebe kuma ya sake tabbatar muku da cewa gwamnati na da dukkanin kayan aiki da kuma yadda za ta iya shawo kan wadannan masu laifi."

Ko dayake shugaban kasar ya sha nanata cewa 'yan bindiga ba su fi karfin gwamnatinsa ba, amma abin takaici ne ganin yadda tsageru masu dauke da makamai ke sanya tsoro a duk fadin kasar tare da hana dalibai ci gaba da karatunsu.

Sai a ranar Alhamis ne Gwamnatin Jihar Neja ta rufe duk makarantun gwamnati saboda rashin tsaro.

Da alama Kaduna za ta dauki matakin da gwamnatocin da suka gabata wadanda suka fuskanci dumbin sace mutane suka aikata. Lokaci yayi da gwamnatin Buhari ya kamata ta zama gwamnatin fadi da cikawa.

KU KARANTA: Kasar Amurka: Mun shirya tsaf domin taimakawa Najeriya kan sace 'yan makaranta

A wani labarin, Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya mayar da martani ga shawarar da Majalisar Tsaro ta Kasa ta yanke na ayyana jihar ta Zamfara a matsayin haramtaccen yanki ga jirage, Daily Trust ta ruwaito.

Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Manjo-Janar Babagana Monguno (mai ritaya), ne ya bayyana hakan a karshen taron majalisar tsaron kasa da aka yi ranar Talata.

Monguno ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya ta hana ayyukan hakar ma’adanai a jihar. Ya ce an dauki matakin ne sakamakon yawaitar rashin tsaro a jihar.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.