Gwamna Zulum ya dauki nauyin karatun 'ya'yan talakawa, 'yan mata 800
- Gwamnan jihar Borno ya dauki nauyin karatun 'yan mata 800 a fadin jihar ta Borno a arewa
- Gwamna ya tabbatar da biyan makudan kudade na makaranta da kuma kayayyakin karatu
- Gwamnan ya shaida cewa, za a ci gaba da biyan kudin makarantar har zuwa kammalawarsu
Gwamna jihar Borno, Babagana Umaru Zulum ya sanya 'yan mata 800 a makarantar gwamnati ta Kwalejin 'Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya (FGGC) dake a garin Munguno.
Gwamnan ya fidda zunzurtun kudi da ya haura Naira miliyan 37 na kudin makaranta, da kuma Naira miliyan 48 don sayen kayan makaranta, littatafai, katifun kwaciya da sauran ababen da ake bukata.
'Yan matan 800, sun kasance 'ya'yan masu karamin karfi da suka fito daga kananan hukumomi 16 na jihar, wadanda galibinsu sun fito ne daga al'ummomin da sukayi fama da hatsarin Boko Haram, inda rikicin ya ki ci ya ki cinyewa.
Tunda aka marabci 'yan matan zuwa FGGC Monguno a wani biki wanda ya samu wakilcin Zulum wanda Maina Yaumi, Sakataren zartarwa na Asusun Bayar da Ilimi na Jihar Borno ya wakilta.
KU KARANTA: Kasar Amurka: Mun shirya tsaf domin taimakawa Najeriya kan sace 'yan makaranta
Mista Yaumi, ya yi kira ga daliban da su kasance masu kwazo, jajircewa da bin doka kuma ya bukace su da su yi karatun ta natsu kasancewar gwamnati a shirye take don daukar nauyin karatunsu zuwa kammalawa.
Ya kara da cewa a wa'adin farko, "Gwamnan ya amince da biyan jimillar kudi N79m na kudin makaranta, kayan sawa, littattafai, katifu, jakunkuna, sandal da sauran bukatun yau da kullun.
"Hakanan, a cikin 'yan makonni kadan, za a sake biyan kudi N80.2m ga makarantar don biyan kudin karatun su na zango nabiyu da na uku."
Ya kara tabbatar wa mutane cewa Gwamna Zulum ya himmatu wajen ganin ya samu damar zuwa makaranta tare da daukaka matsayin ilimi a jihar.
A jawabinta, shugabar Makarantar Aisha Umar Isa Saeed, ta yaba da kokarin Gwamna Zulum tare da yi masa godiya bisa samar musu da daya daga cikin manyan makarantu da ke cikin garin Maiduguri a matsayin wurin aiki na wucin gadi.
Wakilin Gwamnan ya kaddamar da dakin karatun makarantar, wanda Tsohuwar Kungiyar Matan Makarantar ta samar dashi.
KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta fara zaban masu cin gajiyar shirin N-Power
A wani labarin, Wasu 'yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kwashe daliban kwalejin harkar noma da gandun daji dake Mando a cikin birnin Kaduna.
A halin yanzu ba a san yawan daliban da suka sace ba, sai dai kwamishinan harkokin tsaro na jihar, Samuel Aruwan yace yana cikin makarantar kuma suna kan bincike.
Daya daga cikin daliban makarantar ta sanar da BBC cewa cikin dare 'yan bindigan suka kutsa makarantar.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng