Da alamu gwamnatin Buhari bata fahimci matsalar tsaro a Zamfara ba, in ji gwamna Matawalle

Da alamu gwamnatin Buhari bata fahimci matsalar tsaro a Zamfara ba, in ji gwamna Matawalle

- Gwamnan jihar Zamfara ya nuna rashin amincewarsa ga haramtawa jirage bin jihar ta Zamfara

- Gwamnan yace da alamu gwamnatin tarayya ba ta fahimci inane tushen matsalar tsaro a jihar ba

- Ya kuma bayyana cewa, 'yan Najeriya na zuba ido su ga ko matakin zai kawar da matsalar tsaro

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya mayar da martani ga shawarar da Majalisar Tsaro ta Kasa ta yanke na ayyana jihar ta Zamfara a matsayin haramtaccen yanki ga jirage, Daily Trust ta ruwaito.

Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Manjo-Janar Babagana Monguno (mai ritaya), ne ya bayyana hakan a karshen taron majalisar tsaron kasa da aka yi ranar Talata.

Monguno ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya ta hana ayyukan hakar ma’adanai a jihar.

Ya ce an dauki matakin ne sakamakon yawaitar rashin tsaro a jihar.

Da yake mai da martani kan ci gaban da aka samu lokacin da Kayode Fayemi, shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) ya ziyarce shi a ranar Talata, Matawalle ya ce bai tabbata gwamnatin tarayya ta fahimci halin da ake ciki ba.

K KARANTA: Da dumi-dumi: Majalisar dattawa ta tabbatar da nadin sabbin hafsoshin soja

Da alam gwamnatin Buhari bata fahimci matsalar tsaro a Zamfara ba, in ji gwamna Matawalle
Da alam gwamnatin Buhari bata fahimci matsalar tsaro a Zamfara ba, in ji gwamna Matawalle Hoto: Vanguard News
Asali: UGC

“Da alama majalisar tsaro ba ta fahimci inda yanayin matsalolin tsaro a jihar Zamfara take ba amma idan suka yanke shawarar daukar irin wannan mataki to su ci gaba.

“Bana jin tsoron kowace hukuma kuma matsalar rashin tsaro a jihar ta rigayi gwamnatina.

“’ Yan Najeriya suna jiran su ga sakamakon kudurin kwamitin tsaro don ganin ko za a murkushe wadannan ‘yan fashi.

"Idan gwamnatin tarayya ta kasa murkushe su bayan wannan kudurin, to ‘yan Nijeriya za su fahimci cewa sun zauna ne kawai zaman shan shayi, ba wani abu ba,” inji shi.

Ya ce ya fara binciken wadanda suka sace daliban makarantar sakandaren gwamnati ta mata, da ke Jengebe, a Zamfara.

A nasa bangaren, Fayemi ya ce dole ne hukumomin tarayya da na jihohi su yi aiki tukuru don kawo karshen yawaitar satar mutane a kasar.

Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi ne ya raka Fayemi a ziyarar ta zuwa fadar jihar Zamfara.

KU KARANTA: Wike ya sasanta gwamnan jihar Benue da na Bauchi kan batun makiyaya

A wani labarin, Babagana Monguno, mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), ya ce wasu mutane suna amfani da damar tabarbarewar yanayin tsaro a kasar don amfanar kansu, TheCable ta ruwaito.

Da yake magana a ranar Talata bayan taron majalisar tsaron kasa da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta, Monguno ya ce gwamnati ba za ta lamunci lamarin ba. Ya gargadi duk wadanda ke tayar da kayar baya da su daina ko kuma su samu kansu abin zargi.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.